Runduar Sojojin Sama ta Nijeriya ta ce jiragen yaƙinta sun kashe 'yan ta'adda da dama a jihohin Kaduna da Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Edward Gabkwet, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Gabkwet ya ce 'yan ta'addan da suka kashe su ne suka kai hari kwanakin baya a kan fararen-hula tare da sace shanu a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja amma suna zaune ne a dazukan jihar Kaduna.
Ya ƙara da cewa bayanan sirrin da suka tattara sun nuna yadda 'yan ta'addan suke tafiya daga Dajin Alawa na jihar Neja domin komawa mazauninsu Dajin Malum da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
“Daga samun waɗannnan bayanai ne, rundunar sojojin sama ta tsara sannan ta aiwatar da shirinta na kai hari kan maɓoyar 'yan ta'adda a Dajin Malum ranar 21 ga watan Agusta.
“Binciken da aka bayan ƙaddamar da harin da kuma bayanan da muka samu daga mazauna yankin sun nuna cewa an kashe 'yan ta'adda da dama sakamakon samamen," in ji Gabkwet.
A cewarsa, “An kai irin wannan hari a maɓoyar 'yan ta'adda da ke Bayan Ruwa a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
“An bi 'yan ta'addan har cikin ɗakunan da suka gina da kwano a wuri mai cike da ciyayi" inda aka kawar da su.
Gabkwet ya ce luguden wutar da suke yi ta sama, wanda suka sanyawa suna Air Component of Operation Whirl Punch zai ci gaba da gano wuraren da 'yan ta'adda suke tare da kawar da su daga doron ƙasa.