Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya isa kasar Mali domin ganawa da takwaransa Kanar Assimi Goita, a ziyararsa ta farko da ya kai wata ƙasa tun bayan da ya ƙwace mulki a watan Yuli, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rawaito a ranar Alhamis.
Ƙasashen Mali da Burkina Faso da ke maƙwabtaka da Nijar - wadanda su me sojojin da suka ƙwace mulki a shekarar 2020 da 2022 ke mulki a ƙasashen, sun yi alkawarin bayar da hadin kai ga jagororin juyin mulkin Nijar.
A cikin watan Satumba ne kasashen yankin Sahel guda uku suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da ta ƙunshi tanadin kare juna a kan duk wani harin da za a kai kan ɗaya daga cikinsu.
Suna kuma shirin karfafa dangantakar tattalin arziki.
Haka kuma gwamnatocin sun haɗa kai wajen yaƙi da ta'addanci a ƙasashensu.
'Ziyarar ƙawance'
Fadar shugaban kasar ta Mali ta ce Tiani zai yi kwanaki kadan a Bamako babban birnin kasar Mali, kuma zai gana da Goita domin yin ziyarar sa da zumunci da aiki.
Jim kadan bayan ya ɗare kan karagar mulki, Tiani ya yi alkawarin mayar da Nijar mulkin farar hula nan da shekaru uku.
A halin da ake ciki, kasar Mali ta ɗage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a farkon shekarar 2024 har sai baba ta gani.
Kasar Mali na shirin karɓar baƙuncin ministocin ƙasashen uku domin gudanar da taruka da dama a cikin makonni masu zuwa da nufin kawar da cikakkun bayanai kan ayyukan sabuwar kawancen kasashen Sahel, in ji sanarwar a ranar Alhamis.