Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi birnin Berlin na Jamus a ranar Asabar don halartar taron G20 mai hadaka da Afirka, a yayin da yake sonn janyo hankalin masu zuba jari zuwa kasarsa a fannin makamashi da ababen mora rayuwa da habaka kasuwanci, a cewar ofishinsa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron wanda shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya karbi bakunci, zai mayar da hankali ne kan inganta hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasashen Afirka da kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya, G20.
Tinubu zai kuma halarci taron zuba jari na G20 karo na hudu, wanda gwamnatin Jamus za ta dauki nauyin shiryawa, inda zai gabatar da Nijeriya a matsayin kasar da ya kamata a zuba jari a cikinta, in ji Ngelale.
Nijeriya na neman habaka zuba jari ne maimakon dogaro da bashi don farfado da tattalin arzikinta da ke fama da koma baya da dumbin bashi da ake bin ta da hauhawar farashi da karancin kudin kasashen waje da satar danyen man fetur, wanda shi ne babban arzikin da take fitarwa zuwa kasashen waje.