Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta karyata wani labari da aka yada wanda ya ɗaga hankalin mutane inda wasu mutum 14 suka yi zargin cewa an cire musu mazakutarsu a babban birnin kasar, Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN ya rawaito kwamishinan ƴan sandan birnin tarayyar Haruna Garba yana ƙaryata zargin, wanda ya ce an gano ƙarya ne bayan da aka yi wa mutanen gwajin lafiya.
A yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan nasarorin rundunar reshen Abuja, Kwamishina Garba ya ƙara da cewa “a yanzu haka an ɗauki matakin shari’a kan mutum 14 din bayan da aka tabbatar da zargin da suke yi ƙarya ne.
A baya-bayan nan ana ta samun yawaitar ƙorafe-ƙorafe daga mutane da suke zargin ana musu “shafi mulera” ana sace musu mazakuta, ba a Abuja kawai ba har ma a sauran jihohi musamman na arewacin kasar.
Lamarin ya jawo muhawara sosai har a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ƙara jaddada batun, yayin da wasu kuma ke ƙaryatawa.
“A yanzu haka ana tuhumar mutanen da yaɗa labarin ƙarya da neman ɗaga hankulan al’umma,” a cewar kwamishinan ƴan sanda, kan batun mutum 14 da suka kai ƙorafin a Abuja.
“Labarin ƙaryar ya jawo mutane sun so ɗaukar doka a hannunsu kan wasu mutum 10 da suke zargi a babban birnin a makonnin da suka wuce,” in ji kwamishinan.
An samu ƙorafi da yawa
Kwamishinan ƴan sandan Abujan ya ce sun samu aƙalla ƙorafi fiye da 10 mafi yawa daga yankunan Karshi da Gwagwalada da kuma Kwali, inda ya ce a wasu yankunan lamarin ya jawo matasa sun ɗauki doka a hannunsu, sai dai ba a samu asarar rai ba kan hakan.
“Rundunar ƴan sanda ta samu ƙorafi fiye da 10 na zargin sace al’aurar maza a faɗin Abuja, har hakan ya jawo matasa cikin fushi suka dinga ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargin.
“Sai da ƴan sanda suka shiga cikin lamarin wajen mayar da doka da oda don hana rasa asarar rayuka da dukiyoyi.
“An kai mutum 14 da suka ce an sace musu al’aura zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da cewa al’aurarsu na nan ƙalau," kamar yadda CO Haruna ya faɗa
Kwamishinan ƴan sandan ya yi kira ga mutane da su guji ɗaukar doka a hannu don kar a kashe ko jikkata wanda bai ji ba bai gani ba.