Hukumomin Nijeriya sun yi gargadin cewa za a iya fuskantar mamakon ruwan sama hade da ambaliyar ruwa a kasar, inda suka bukaci mutane su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da daukar matakan gaggawa da suka dace.
Hukumomin da ke kula da yanayi da muhalli sun ce wannan abu zai faru ne daga tsakanin ranar 13 zuwa 18 ga watan Satumba, amma ana sa ran zai fi tsanani daga 17 zuwa 18 ga wata.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Manzo Ezikiel ya shaida wa TRT Afrika cewa wannan sanarwar ta fito ne daga Hukumar Kula da Yanayi ta kasa NIMET, da ke dubawa tana ganin yawan ruwan saman da aka yi lokaci zuwa lokaci.
“Da muka gano wannan shi ne muka fara wayar da kan jama’a don su zama cikin shirin daukar matakai na kare kansu a kan lokaci.”
Ita ma Ma’aikatar Muhalli ta kasar a sanarwar da ta fitar ranar Laraba ta ce an yi hasashen cewa akalla jihohi 15 daga cikin 36 na kasar ne za su fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai jawo ambaliyar ruwa a yankuna da kuma wuraren da ke da manyan gonaki.
“Sakamakon karuwar yawan ruwa a Kogin Binuwai da Kogin Neja, muna kira ga al’ummomin da ke zaune a kusa da wadannan koguna har zuwa jihar Bayelsa da su dauki matakan da suka dace,” in ji ma’aikatar.
Matakan NEMA
Ba wannan ne karo na farko ba da ake fitar da irin wannan sanarwa ba, a watan da ya gabata ma hukumar NEMA ta fitar da irinta, to ko wadanne irin matakai hukumar ke dauka?
Ezekiel ya ce “Da farko muna fitar da wannan magana ne don mutane su gane yanayin abin da zai iya faruwa a kusa da su ko tare da su.
"Ka ga kenan idan matsala za ta zo ko aka fada wa mutum ga matsala mai zuwa, to an riga an shirya shi yadda shi ma zai zama a shirye. Idan lamarin na gudu ne ya gudu,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa “Abu na biyu shi ne, irin wannan sanarwar da muka fitar, ba wai mun fitar da ita farat daya ba ne, da ma tana cikin shirye-shiryenmu na yanayin magance ambaliyar ruwa ko shawo kanta tun farkon shekara.
“Ko yanzun nan da muke magana muna da ma’aikatanmu a ofisoshinmu na shiyya wadanda an riga an tura su zuwa garuruwa daban-daban don wayar da kan mutane kan abubuwan da suka kamata su yin a daukar matakai.”
Mai magana da yawun hukumar ta NEMA ya kuma ce hukumarsu tana hulda da gwamnatocin jihohi saboda wasu mutanen da yawa ba sa samun labara, don haka hakkin gwamnatin jiha ne ta kwashe mutane zuwa wurare masu tsaro.
“Kuma a yanzu haka muna da sakonnin sauti da bidiyo a rediyo da talabijin don wayar da kan mutane kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa don sanar da mutane matakan da za su ceci rayuwarsu,” in ji Ezekiel.
Ezekiel ya ce a duk gargadin da ake bayarwa a baya tun farkon damina, wannan ya fi karfi saboda ana cikin watan Satumba inda aka fi tafka ruwan sama.
“Saboda haka duk shirye-shiryen da ake kan ambaliyar ruwa, wannan ne lokacin da kowa zai dauki mataki.”
Karancin abinci
Wani kwararre a kan harkar noma kuma farfesa a fannin noma, Ebenezer Arifalo ya ce daga cikin illolin ambaliyar ruwa akwai yadda yake lalata gonaki da shuka.
Ya yi gargadin cewa tasirin ambaliysar ka iya ta’azzara wahalhalun da manoma ke ciki da wanda ‘yan Nijeriya je ciki na talauci da rushewar tattalin arziki.
“Ana fuskantar matsalar karancin abinci saboda mamakon ruwan sama da ambaliya da tuni suke faruwa a wasu sassan kasar," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Turkiyya, Anadolu.
Lamarin zai shafi gonakin shinkafa da na hatsi a jihohin arewacin kasar, sannan manoma da dama da suka ci bashi don yin nom aka iya tafka babbar asara,” ya kara da cewa.
Yawanci akan samu ambaliyar ruwa a Nijeriya daga watan Mayu har zuwa Satumban kowace shekara.