Ana sa ran sabon “Kudurin Malaman Afirka” zai kawo sauyi mai kyau da cigaba a wajen mu’amala da zamantakewa ta fannin addini a nahiyar, kamar yadda limamin masallacin kasa na Nijeriya, Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari ya faɗa.
An gabatar da kudurin ne a taron koli na Malaman Afirka na shekara-shekara karo na 5 da Majalisar Gidauniyar Mohammed VI ta shirya a Maroko, a makon da ya wuce.
Kudurin mai taken “Kudurin Malaman Afirka” yana magana ne a kan yadda ya kamata zamantakewa ta kasance tsakanin malamai, da alaƙar Musulmai da wanda ba Musulmi ba, da kuma koyar da girmamawa da mutuntawa a tsakanin al’umma.
Sheikh Maqari wanda yana daya daga malamai 12 na tawagar Nijeriya, ya ce babban abin da ya fi alfanu game da ƙudurin shi ne tabo batun bai wa malaman Afirka damar fitar da fatawowi a kan abin da ya shafe su, ba sai sun jira wasu yankunan ba.
“Ya kamata a ce duk matsalolinmu na Afirka, malamanmu za a dinga tuntuba su samar mana da mafita, ba wai a ce ana shigo mana da fatawowin da ba za su yi daidai da yanayin Afirka ba,” a cewar Farfesa Maqari.
Malamin ya ce hakan ba yana nufin ba za a ƙara ɗaukar kowace fatawa daga ko ina ba, sai dai ya danganta da dacewarta.
“Ita da ma fatawa ana so a kalle ta ta abubuwa guda biyu, wato waje da lokaci. Tana sauyawa gwargwadon waje da lokaci. Kamar yadda aka sani, zamani da yanayin waje duk suna mata tasiri.
“Babu yadda za a yi mutumin da ya rayu a Afghanistan ko a Rasha, ya zo ya yi fatawa a kan zamantakewar al’umma r Afirka, kuma ta dace da mutanen Afirka".
“Ba zai yiwu ba, saboda yana bukatar ya san yanayin zamantakewar Afirka kafin ya san irin fatawa kan abin da ya shafi Afirka. Wannan shi ne abin da muke fada,” malamin ya jaddada.
Malamin ya ce a yanzu ana bukatar mutane su je su yi bitar ƙudurin don a fahimce shi sosai, sannan a samu mabambantan fassarori, daga nan sai a ga ta yaya za a mayar da wannan ƙuduri zuwa aiki.
Kazalika ya ce tun da kowace ƙasa tana da cin gashin kanta, to a yanzu za su je su duba su ga ta yadda ya dace su aiwatar da ƙudurin, don yin daidai da nasu yanayin zamantakewar.
Mene ne taron ƙoli na malaman Afirka?
Gidauniyar Sarki Mohammed na 6 ne ke shirya taron duk shekara, da nufin samar da ƙudurin da zai zamewa malaman da ke ƙarƙashin gidauniyar jagora, wajen tabbatar da manufofin ƙungiyar a hukumance.
Taron na kwana biyar da aka yi daga Litinin 3 ga Disamba zuwa Juma'a 8 ga Disamban 2023, ya samu halartar malamai fiye da 300 daga kasashe 48 na Afirka, inda malamai biyu zuwa uku ne suka halarta daga kowace ƙasa.
Sai dai daga Nijeriya, tawaga mai malamai 12 ne suka halarta, karkashin jagorancin Farfesa Sani Zahradden, babban limamin Jihar Kano.
Ita dai wannan ƙungiya ba ta ginu a kan wata aƙida ɗaya ba. Hakan ne ma ya sa malamai daga mabambantan aƙidu daga Nijeriya suka halarci taron, in ji limamin na Masallacin Kasa na Abuja.
Ana zabar malaman da ke halartar taro ne bisa cika sharuɗɗan malanta, ko kuma wadanda suka je saboda wakilci na wata ƙungiya.
Sheikh Maqari ya ce malaman da suka je daga Nijeriya sun haɗa da mambobi daga dukkan sassan Nijeriya, na arewaci da kudancin ƙasar.