Rundunar sojin Nijeriya ta ƙaryata batun da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai cewa ‘yan ta’adda sun ƙwace wani sansanin horar da sojoji a garin Kontagora na jihar Neja.
“Wannan iƙirari ne mara tushe da ya jawo rashin kwanciyar hankali a tsakanin al'ummar Kontagora da Mariga, da kuma jihar Neja baki ɗaya,” in ji sanarwar da rundunar mai ɗauke da sa hannun daraktanta na watsa labarai Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Laraba a shafin X.
Ta ci gaba da cewa “Sai dai muna so mu fayyace cewa babu wata barazana da ta tabbata a wadannan yankuna kamar yadda ake yaɗawa, saɓanin bayanan da Honorabul Abdullahi Isah mai wakiltar mazaɓar Kontagora II ya gabatar a zauren majalisar dokokin jihar Neja a ranar 28 ga watan Oktoba 2024.”
Rundunar sojin ta ce rahotannin da ke nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai farmaki a yankin na horar da sojoji da kuma korar mazauna unguwanni 23 da ke faɗin Kontagora da Mariga, “ba gaskiya ba ne, illa yaudara domin da alama an ƙirƙire shi ne don tayar da hankula a yankin.”
Sojojin sun ce wani bincike da sashen leƙen asirin rundunar ya yi ya tabbatar da cewa mutanen da aka gani a yankin makiyaya ne da ke neman wuraren kiwo, kuma ba a gano mugun nufi ko wani mummunan aiki a tare da su ba.
“A yayin da muke jin daɗin yadda al’umma ke taka-tsantsan da kuma sadaukarwa mai girma ta ɗan majalisar, muna kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su tunkari irin wannan lamari cikin taka-tsan-tsan tare da tabbatar da bayanai daga rundunar sojojin Nijeriya, a irin wannan yanayi,” in ji Manjo Janar Nwachhukwu.
Rundunar ta kuma yi gargaɗi cewa akwai yuwuwar sanya tsoro mara dalili da haifar da firgici da karkatar da albarkatu masu mahimmanci daga ainihin abubuwan da suka fi dacewa da tsaro, da kuma dagula yanayin tsaro, idan ba fahimci irin wannan yanayin ba.
Ta ce sansanonin horonta sun kasance amintattu, masu ƙarfi, da aka tsara su don kawar da duk wata barazanar tsaro cikin sauri.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa tana ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijeriya baki ɗaya.