Tawagar karshe ta sojojin Faransa za ta kammala ficewa daga Jamhuriyar Nijar a yau Juma’a, abin da ya kawo karshen fiye da shekaru goma da suka kwashe suna yaki da masu ikirarin jihadi a kasar.
Ficewar dakarun Farana ta bar daruruwan sojojin Amurka da gomman sojojin Italiya da na Jamus a kasar ta Nijar.
Faransa ta ce za ta kwashe dakarunta kusan 1,500 da suka hada da matukan jiragen yaki daga Nijar bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninta da sojoin kasar wadanda suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Wannan ne karo na uku cikin watanni 18 da aka kori dakarun Faransa daga wata kasa a yankin Sahel.
An tilasta musu ficewa daga Mali da Burkina Faso a farkon wannan shekarar bayan sojoji sun yi juyin mulki a kasashen biyu.
Dukkan kasashen uku suna yaki da kungiyoyi masu ikirarin jihadi wadanda suka kaddamar da hare-hare a arewacin Mali a 2012, sannan daga bisani suka shiga Nijar da Burkina Faso.
Jerin juye-juyen mulkin da aka yi a yankin tun daga 2020 ya sanya dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da kasashe da ta yi wa mulkin mallaka, abin da ya bai wa Rasha damar yaukaka dangantaka tsakaninsu.