Jirgin farko ya sauka a Abuja ne da misalin karfe biyun dare. Hoto/Channel TV

Jiragen farko dauke da ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga kasar Sudan sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport da ke Abuja ranar Laraba da tsakar daren.

Jumullar dalibai 354 ne jiragen suka dauko daga filin jirgin saman birnin Alkahira na Masar.

Jirgin sojin Nijeriya samfarin C 130 ya debo dalibai 80, sai kuma jirgin kamfanin Air Peace ya kwaso 274.

Jirgin farko ya sauka a Abuja ne da misalin karfe biyun dare.

Manyan jami'an gwamnatin Nijeriya da suka hada da Ministar Ma'aikatar Agajin Gaggawa da Jinkai, Sadiya Farouk ne suka tarbi daliban.

A lokacin da take jawabi, Hajiya Sadiya ta ce gwamnati za ta bai wa kowanne mutum N100,000 domin ya samu damar kla da kansa.

Daliban na Nijeriya sun shafe kwanaki kan iyakar Sudan da Masar sakamakon matakin da kasar ta dauka na kin bude iyakarta domin su wuce.

Sai dai bayan Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya sa baki da kuma taimakon Shugaba Abdel Fattah El-Sisi na Masar, hukumomi sun bude iyakar.

Gwamnatin Nijeriya da tabbatar da cewa za ta yi kokarin dauko duk wani dan kasar da ke Sudan muddun yana son komawa gida.

Rikicin na Sudan, wanda ake yi tsakanin sojin kasar da dakarun RSF, ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da jikkata dubbai.

Kazalika rikicin ya sanya kasashen duniya suna kwashe 'ya'yansu saboda fargabar abin da ka je ya komo.

A makon jiya ne hukumomi suka ce an hana 'yan Nijeriya da wasu kasashe da suka kai 7000 tsallakawa zuwa Masar don isa inda jirage za su kwashe su don kai su kasashensu.

Tsaka-mai-wuya

Tun da farko daliban sun yi layi don shiga bas-bas da za su dauke su zuwa Masar. Hoto/ @nidcom_gov

Tun da farko daliban Nijeriya sun rika korafi game da mawuyacin halin da suka shiga a Sudan tun da aka soma rikicin inda suka yi zargin cewa hukumomi sun ki kwaso su zuwa gida.

Daga bisani gwamnatin kasar ta hannun hukumar NEMA ta bayyana cewa ta samar da motocin bas-bas guda arba'in domin kwaso daliban.

“Tawagar motoci 13 da ke dauke da kashin farko na wadanda aka kwaso daga Khartoum na kasar Sudan tana tafiya zuwa yankin Aswan na kasar Masar kuma daga nan jirgi zai dauke su zuwa Nijeriya,” in ji NEMA.

Sai dai daga bisani daliban sun wallafa bidiyoyi a soshiyal midiya inda suka rika korafi kan yadda motocin da suka debo su suka lalace a dokar-daji.

TRT Afrika da abokan hulda