Miliyoyin Musulmai a Nijeriya na cike da fargabar fara azumin watan Ramadan a yayin da ake ci gaba da shan fama wajen samun kudi lakadan don hada-hadar yau da kullum a kasar.
A ranar Alhamis ne al’ummar Musulman duniya za su fara ibadar ta tsawon wata daya, sai dai duk da cewa ‘yan Nijeriya da dama sun fara sabawa da rashin kudi lakadan, da yawa na bayyana fargaba kan yadda za su dinga sayen abubuwan yau da kullum ba tare da isassun kudi a hannu ba.
“Ba watan da nake so irin na azumi a rayuwata, amma Allah Ya sani ina cike da fargabar yadda za mu yi cikin wannan tsanani na rashin kudi, saboda dole akwai kayan masarufin da kullum ne muke bukatar sayensu,” in ji wani magidanci Malam Tijjani a hirarsa da TRT Afrika.
A watan Oktoban bara ne Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da sauya fasalin kudaden naira, kuma a watan Janairun 2023 wa’adin daina amfani da tsoffin kudin ya cika. Sai dai hakan ya jefa miliyoyin kasar cikin halin ni ‘yasu inda al’amuran saye da sayarwa suka kusa tsayawa cak.
Duk da cewa sau biyu ana kara wa’adin daina amfani da kudaden, sannan kuma Kotun Kolin kasar ma ta dage wa’adin inda ta ce a ci gaba da kashe tsoffin har sai 31 ga watan Disamba, hakan bai sa tsoffi da sabbin kudaden sun wadata kamar da ba.
Kiraye-kiraye
Malaman addinin Musulunci da dama sun yi ta kiraye-kiraye a hudobinsu gabanin fara azumi cewa ya kamata CBN ya saki takardun naira isassu don Musulmai su sami sauki a yayin Ramadan.
Musulmai su ne kashi 51 cikin 100 na yawan al’ummar Nijeriya kuma da yawan su kamar Malam Tijjani, na zaune ne a kauyka inda mutane ba su waye da tsarin takaita hada-hadar kudade a hannun jama’a da gwamnati ke ta fatan samarwa ba.
Sannan kuma Nijeriya kasa ce da kashi 40 cikin 100 na al’ummarta ba su da asusun ajiya na bankuna.
“Ni manomi ne kuma karamin dan kasuwa wanda sana’ata ta ta’allaka ne a kan saye da sayarwa nay yau da kullum, sannan akwai abubuwan bukatar da dole kullum ne muke sayensu don ba mu da arzikin saya da yawa mu jibge, sannan abokan cinikin ba su san ma wani abu ATM ko POS ba kuma ba su da asusun banki.
“To ta yaya ake tunanin za mu ji dadin rayuwarmu a wannan wata mai tsarki na azumi? Ta yaya za mu sayar mu kuma sayi abincin da muke bukata na sahur da buda baki?,” Malam Tijjani mazaunin garin Yana a jihar Bauchi, arewa maso gabashin Nijeriya, ya fada cikin korafi.
Ba mutanen karkara kawai ke irin wannan korafi ba, wayayyu mazauna maraya ma suna ci gaba da sukar gwamnati kan wannan “tsattsauran mataki da ya saka mutane a tasku.”
Wani fitaccen mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Farfesa Jibrin Ibrahim ma a ranar Laraba, jajibirin azumi ya wallafa sako zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan CBN a shafinsa na Tuwita, yana tambayarsu yaushe wannan dawainiya za ta zo karshe.
“Zuwa ga @MBuhari da @GodwinEmefiele, haka za mu ci gaba da rayuwa babu naira lakadan kuma cikin tattalin arzikin da ke durkushewa har zuwa 29 ga watan Mayu?”
Mutane da dama sun sake wallafa sakon farfesan wasu kuma sun yi ta tsokaci a kai, suna bayyana fargabarsu ta fara azumi a cikin “mummunan yanayi na rashin kudi lakadan.”
An yi amannar cewa mata ne a kan gaba wajen tsara al’amuran maraba da azumin watan Ramadan a gidaje, musamman ta fannin abin da za a ci.
TRT Afrika ta yi magana da wasu daga cikinsu daga kauyuka da birane, kuma duka sun bayyana yadda fargaba ta mamaye sun a yadda za su fara azumi cikin rashin isassun kudi lakadan.
Fadila Bashir wata mazauniyar birnin katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta bayyana lamarin da cewa “ya ma dan fi sauki a birane maimakon kauyuka.”
“A kalla mu a nan akwai bankuna da za a yi aika kudi don sayen kaya ko a yi amfani da POS ko ATM ba kamar kauyuka ba.
Sai dai duk da haka a nan din ma muna cin kwakwa don kafin ka aika kudi ko a cira a POS sai matsalar rashin kyakkyawan ya kusa haukata mutum.
“Taransufa ba ta tafiya, idan ta ATM ko POS za a aika su ma ba sa tafiya, kuma ko kwarar gero babu mai ba ka sai an ga shigar kudin. Wallahi wani lokacin wannan tashin hankalin kawai ya isa ya sa jininka ya hau,” in ji ta.
'Kudina kamar ba nawa ba'
Ta ci gaba da cewa "yanzu a misali kankara da ake tsananin bukatarta lokacin azumi musamman da zafin nan, sayenta kudi hannu ne. Ba za su yarda ka sai kankarar 100 ka musu taransu fa ba."
Ita ma Samira Ciroma duk da rufin asirin da Allah ya yi mata ta nuna damuwa a kan yadda za ta dinga sayen naman da za ta a abincin azumi don farfesun buda baki.
“Ai dole na damu don masu sayar da naman ba sa yarda da wata taransufa kuma ba sa amfani da POS. Idan banki ka je don cire kudin ma babu. Ina ga bana dai da hakuri za mu yi azumin nan.”
A can baya idan aka fara hada-hadar fara azumi kasuwanni kan cika da mutane a yankunan da Musulmai suka fi yawa, amma a bana abin ya sauya don kuwa babu mutane sosai kamar yadda aka saba gani, kamar yadda Malam Uzairu Bala na kasuwar Singa da ke Kano ya fada.
Aliyu Musa na daga cikin mutanen da suka ce damuwar wannan yanayi ta sa ba su da abin cewa da ya wuce gode wa Allah.
Magidancin mai mace daya da ‘ya’ya bakwai ya ce “Ina da kudi a asusun bankina, amma sun zama kamar ba nawa ba. Ba abin da zan iya yi da su. Ga shi gobe ne azumi ba ni da ko sisin da zan sayo mana mahadin abincin sahur.
“Mai shagon unguwarmu da yake ba ni bashin kaya na kai gejina, yau kwana uku ina so na tura masa kudadensa don na samu ya ban sabon bashi amma lamarin sabis din nan ya hana.
"Allah kadai Ya san yaya batun sahur zai kasance a yau,” Malam Ali ya gaya min cikin kakabi.
Daya damuwar da Hajiya Samira ke da ita ita ce ta yadda lamarin nan ya sa a yanzu ba ta iya yi wa ‘yan matan da ke kai mata tallar albasa daga kauyukan da ke kusa da Sokoto ciniki.
“Yaran nan da iyayensu ba su san komai da ya shafi lamarin hada-hadar kudi a zamanance ba, abin da suka sani shi ne kawai su girbe amfanin gonarsu su kai birane su sayar.
“A yanzu idan suka zo gidana talla tausayi suka ba ni saboda sai na ga da kyar suke sayar da kashi daya bisa shida na kayan. Jiya ma sun kawo tallar albasa kuma ina son saya don sirin azumi amma haka nan ni da su duk muka hakura.
“Sun ce ba wanda ya sayi albasarsu tun safe da suke gararambar talla a cikin birni, kuma da alama haka suka koma da ita gida,” Samira ta fada.
Kwararru a fannin tattalin arziki na jin tsoron cewa irin wannan yanayi na rusa tattalin arziki tare da durkusar da masu kanana da matsakaitan sana’o’i.
Musulmai da dama a kasar sun yi amannar cewa azumin bana ga alama sai ya fi na shekarar 2020 wahala, wanda aka yi shi a cikin tsananin kullen annobar cutar korona.