Ana magana da sama da harsuna 500 a Nijeriya, sai dai an fi magana da Hausa da Igbo da Yarabanci. / Hoto: Adedeji Odulesi

Daga Abdulwasiu Hassan

Harshe daban, bangare ne na wata rayuwa daban, kamar yadda kwararre kan harsuna na kasar Italiya Federico Fellini ya bayyana. Wannan ne abin da Adedeji Odulesi ke tallatawa.

Dan Nijeriya ne mai magana da harsuna da dama kuma fitacce a kafafen sada zumunta wanda kaunar da yake yi wa magana ta dace da son da yake yi wa harsuna – inda ya iya Hausa da Yarabanci da harshen Igbo da Pidgin da Sifaniya da Faransanci da Jamusanci.

A cikin ƙasa mai mutane miliyan dari biyu waɗanda ke magana da harsuna sama da 500, za a yi tsammanin magana da juna za ta kasance daban kamar al’adun Nijeriya. Adedeji na kawo duka wadannan da kuma karin da dama zuwa shafinsa na Facebook, inda yake da akalla mabiya mutum dubu 86.

Adedeji wanda dan asalin Jihar Ogun ne da ke Kudancin Nijeriya, na kiran kansa “mai jin harsuna da dama wanda ake yayi wanda yake wa sauran irinsa murnar iya harsuna da dama”, baya ga aikin da yake yi na mai gabatarwa a wuraren bukukuwa wato MC.

Yana amfani da irin tattaunawar da yake yi da mutane – tun daga kan wani soja wanda ke iya magana da harsuna bakwai da karin harshe da dama da wata Banufiya da ke magana da harsuna Nijeriya biyar – inda yake yin hakan don inganta fahimtar juna tsakanin kabilu daban-daban da suke a kasar.

Amfani da harshe wurin hadin-kai

Akasarin tattaunawar da Adedeji yake yi ba su da tsawo kuma yana yin su ne ba tare da kambama su ba, inda yake ba wadanda yake hirar da su damar yin magana da harsuna daban-daban tare da jefa musu tambayoyi a harsuna dayawa domin bai wa masu kallo damar fahimtar fasahar magana da harsuna da dama.

Adedeji ya bayyana cewa fahimtar harsuna da dama na sa mutane su koyi hakuri da juna. / Hoto: Adedeji Odulesi

Na gano ba da daɗewa ba bayan farawa cewa yawancin bakina suna da abu iri daya: shi ne abin da mutum zai kira 'makantar kabilanci'.

Suna ganin dukan mutane a matsayin ’yan’uwansu maza da mata,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. Daya daga cikin hirarrakinsa da ta shahara ita ce wadda ya yi da Ibrahim Isau, wani sojan Nijeriya.

Mutum dubu 7.3 suka so tattaunawar sannan mutum dubu 1.7 suka tofa albarkacin bakinsu sannan mutum 1,73,000 suka kalla. Haka kuma akwai wata hira da ya yi da wani mai jin harsuna da dama wato Rabiu Safiyanu Liman wadda sama da mutum 500,000 suka kalla.

Ta yaya Adedeji ya soma son harsuna inda daga baya hakan ya kasance aikin da yake yi.

“A lokacin da nake tasowa, bana so ana cewa ni Ijebu ne. Abin da nafi jin zafinsa shi ne a lokacin da wata budurwa ta guje ni saboda ni Ijebu ne,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“A shekarar 2019, shekaruna sun kai na zama cikakken matashi. Na jagoranci bikin bayar da kyaututtuka na Deeper Life. Na fito na shaida wa duniya cewa ni Ijebu ne... Bidiyon ya yadu inda aka neme ni domin aikin MC.

A matsayin mai jin harsuna da dama, Adedeji ya bayyana cewa irin dadin da yake ji na mutane da ke iya magana da harsuna da dama ne ya ba shi karfin gwiwar soma yin hira da su. Babban sako a cikin duka shirye-shiryensa shi ne koyon harsuna da dama na sa jama’a su koyi hakuri da juna.

“A lokacin da ake koyon harshe, mutum na koyon wata sabuwar al’ada wadda ke da alaka da ita inda mutum a hankali zai iya koyonta,” in ji shi.

A Nijeriya, Hausa da Yarabanci da Igbo su ne harsunan da aka fi magana da su a kasar, inda ake amfani kuma da Turanci domin hada kan masu amfani da harsunan.

“Bolanle Wasiu na daya daga cikinsu. Ta fito ne daga Ibadan, inda take dauke da zane a fuska. Ta iya magana da harshen Yarabanci da Igbo sosai,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

“Haka kuma akwai Safiyanu Liman, wanda wani Bahaushe ne daga Kano wanda aka haife shi a Ekiti kuma yake magana da Hausa da Yarabanci da Ekiti da Ingilishi. Shi ma wani mutum ne mai burgewa.”

A cikin duka masu magana da harsuna da dama da ya hadu da su a shafinsa na Facebook, ya ce Ibrahim Isau daga Jihar Kogi shi ne ya fi “burge” shi.

Isau na magana da Hausa da Igbo da Ibibio da Yarabanci da Isoko da Igbira da Pidgin da sauran harsunan Nijeriya.

Adedeji na karbar bakoncin mutane daga bangarori daban-daban na rayuwa a shirinsa: / Hoto: Adedeji Odulesi

Akasarin mabiyan Adedeji suna shaida masa cewa bidiyoyinsa na ba su kwarin gwiwa domin mayar da hankali domin koyon sauran harsuna.

“Na yi mamaki kan yadda wani Bahaushe ya rubuto mani kan cewa yana samun kwarin gwiwa sakamakon hirarrakina, shi da wasu sun hada wani group a Facebook domin koyon Yarabanci,” kamar yadda ya bayyana.

“Suna da malamai wadanda ke bayar da gudunmawa a group din. Lokaci na karshe da na ji daga gare su, suna da mambobi kusan 1,000 wadanda suka fito daga kabilu daban-daban duk a yunkurinsu na koyon Yarabanci.”

Kamar yadda Adedeji ke yawan yin kirari a karshen ko wace tattaunawa, “Nijeriya daya!”

TRT Afrika