Nyesom Wike ya sha alwashin kawo gagarumin sauyi ga birnin tarayya./Hoto: Nyesom Wike/Facebook

Ministan Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Nyesom Wike, ya sallami shugabannin manyan hukumomi da ma'aikatun Abuja ashirin da daya.

Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Anthony Ogunleye, mai magana da yawun ofishin ministan, ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ba ta fadi dalilan da suka sa ministan ya kori shugabannin ma'aikatun ba. Sai dai tun da aka nada shi a mukamin minista, Mr Wike ya sha alwashin yin garambawul ga ma'aikatun birnin.

Ta kara da cewa an umarci mutanen su mika ragamar ofisoshinsu ga daraktoci mafi girman mukamai na ma'aikatunsu, tana mai cewa nan ba da jimawa za a maye gurbinsu.

Labari mai alaka: Nyesom Wike: Shin tsohon gwamnan Ribas zai iya kawo sauyi a Abuja?

Kazalika ya ce zai kawo gagarumin sauyi a birni na Abuja, wanda ya ce ana keta doka a fannoni daban-daban. Hasalima tuni Mr Wike ya soma rusa wasu gine-gine a birnin na Tarayyar Nijeriya, wadanda ya ce an yi su ba bisa ka'ida ba.

Ga jerin ma'aikatun da ministan na Abuja ya kora daga aiki:

  • Kamfanin Zuba Jari na Abuja

  • Hukumar Kula da Kasuwannin Abuja

  • Hukumar Sufuri ta Abuja

  • Hukumar Samar da Ci-gaban Gidaje da Gine-Gine ta Abuja

  • Kamfanin Ci-gaban Fasaha na Abuja

  • Ma'aikatar Fina-finai ta kasa da kasa da ke Abuja

  • Kamfanin Powernoth AICL Equipment Leasing Ltd

  • Hukumar Watsa Labarai ta Abuja

  • Hukumar Abuja Enterprise Agency

  • Hukumar Samar da Ruwa ta Abuja wato FCT Water Board

  • Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Abuja

  • Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Abuja

  • Hukumar Kula da Asibitoci ta Abuja

  • Hukumar Kula da Muhalli ta Abuja

  • Hukumar Bayar da Tallafin Karatu ta Abuja

  • Hukumar kula da Kiristoci Masu zuwa Ziyara wurare masu Tsari

  • Hukumar Aikin Hajji ta Aabuja

  • Cibiyar Abuja Infrastructure Investment

  • Hukumar Inshorar Lafiya ta Abuja

  • Ma'aikatar da ke Kula da Garuruwan da ke Kewayen Abuja

  • Majalisar Kula da Cikin Birnin Abuja

TRT Afrika