Farfesa Mojisola  ta ce NAFDAC ba ta yi wa  taliyar Indomie ta 'Special Chicken Flavour' rajista ba. Hoto/NAFDAC

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya, NAFDAC, ta ce ranar Talatar nan za ta soma gwaji kan ingancin taliyar Indomie a fadin kasar.

Ta bayyana haka ne sakamakon rahotannin da ke cewa taliyar na dauke da sinadarin ethylene oxide wanda ke haddasa cutar daji.

A wata sanarwa da ta fitar, Shugabar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce: “Sashen da ke kula da ingancin abinci na hukumarmu zai fara gwaji kan taliyar Indomie a ranar 2 ga watan Mayun nan.

“Abin da ake son dubawa shi ne sinadarin ethylene oxide. Tuni an bai wa daraktan kula da dakunan gwajin abinci wannan aikin. Yana aiki kan fayyace bayanan da aka tattara,” in ji ta.

Farfesa Mojisola ta ci gaba da cewa “Dama dai an san cewa an dade da hana shigar da Indomie kasar tsawon shekaru da suka wuce. Tana daya daga cikin jerin abincin da gwamnati ta haramta shiga da su. An haramta ta a Nijeriya kuma NAFDAC ba ta yi mata rijista ba.

Shugabar ta NAFDAC ta ce abin da suke yi a yanzu shi ne sake yin taka-tsantsan don tabbatar da cewa ba a shigar da taliyar cikin kasar ta haramtacciyar hanya ba, “idan kuma har an yi hakan, to jami’anmu da ke sa ido za su gano ta."

Baya ya ga haka, NAFDAC za ta tabbatar da cewa an yi gwaji kan yaji da sinadarin dandanon Indomie da na sauran taliya irin ta a Nijeriya.

“Wannan shi ne aikin da jami’an NAFDAC za su yi a wannan makon a cikin kamfanoni da kasuwanni. Kuma za a sanar da al’umma sakamakon dukkan binciken," a cewarta.

NAFDAC ba ta yi wa 'Special Chicken Flavour' rajista ba

A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na Twitter, NAFDAC ta ce ba ta yi wa taliyar Indomie ta 'Special Chicken Flavour' rajista ba.

"Akwai bukatar a san cewa taliya na daga cikin jerin abubuwan da gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta haramta shiga da su, hakan na nufin ba a yarda a rika shigar da ita Nijeriya," a cewar sanarwar.

Tun a karshen makon jiya ne rahotanni suka fara watsuwa cewa hukumomin lafiya na kasashen Malaysia da Taiwan sun gano sinadarin da ke jawo cutar kansa a cikin taliyar Indomie mai dandanon.

Wannan lamari ya sa wasu kasashen duniya musamman inda taliyar wacce asalinta daga kasar Indonesiya ne, ta fi karbuwa suka fara daukar matakai.

Hukumomin lafiya na kasashen Malaysia da Taiwan ne suka fara gano sinadarin da ke jawo cutar kansa a cikin taliyar Indomie / Hoto: Indomie.com
TRT Afrika da abokan hulda