Jakadan Amurka a Nijeriya ya kai ziyara ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya:Hoto/X/Bianca Odumegbwu-Ojukwu

Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta yi kira ga mahukunta a Amurka su bi tsare-tsaren da ake da su idan suka tashi mayar da baƙin-haure daga ƙasarsu zuwa Nijeriya.

Ta yi wannan kiran ne ranar Lahadi a Abuja, bayan jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills Jr ya kai ziyara Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito.

Ta bayyana irin fargaba da matsalar kuɗin da ‘yan Nijeriya da ke Amurka ke fuskanta tun lokacin da gwamnatin Amurka ta ce za ta kori wasu baƙi.

“Ga sabuwar gwamnatin Amurka, muna son a yi mana alƙawari. Idan za a dawo da mutane, a dawo da su cikin mutunci,” in ji Odumegwu-Ojukwu.

Ta bayyana cewa kimanin ‘yan Nijeriya 201 ne ke sansanonin hukumar shige da ficen Amurka yayin aka yanke shawarar mayar da 85 daga cikinsu.

“Shin za a ba su lokacin damar sarrafa ƙadarorinsu ko kuma za a tura su cikin jirage ne kawai a dawo da su?” in ji ta, tana mai jaddada irin damuwar da tasa ƙeyarsu za ta janyo.

Ta ce dawo da mutanen zai shafi waɗanda ake dawowa da su da kuma ‘yan'uwansu a Nijeriya waɗanda suka dogara ga abin da suke trurowa domin rayuwa da karatu.

Odumegwu-Ojukwu ta jaddada buƙatar bi da waɗanda za adawo da su cikin mutunci kuma a ba su damar daidaita lamurransu kafin su dawo.

Ta ce sama da ‘yan Nijeriya 14,000 suke karatu a Amurka inda iyaye ke fargaba game da yiwuwar sauya tsare-tsaren izinin zama a Amurka.

A nasa jawabin, jakadin Amurka a Nijeriya, Richard Mills Jr ya ce duk ‘yan Nijeriya da za a mayar da su ƙasar za a sauƙe su ne a Legas maimakon a kai wasu Abuja ko Fatakwal.

“Rukuni na farko zai ƙunshi waɗanda kotu ta samu da laifi da kuma waɗanda suka saɓa wa dokokin shiga Amurka. Wasu sun ɗaukaka ƙara, amma an hana su kuma dole su bar ƙasar,” in ji Mills.

Ya tabbatar da jajircewar Amurka wajen ƙarfafa dangantakar cinikayya da Nijeriya, yana mai cewa, “wannan gwamnatin za ta fi mayar da hankali kan cinikayya da kasuwanci domin ɗorewar dangantakarmu mai ƙarfi.”

TRT Afrika