Wata mummunar ambaliyar ruwa da aka yi a Maiduguri ta rusa katangar wani gidan yari a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya a farkon makon da ya gabata, lamarin da ya bai wa fursunoni 281 damar tserewa, in ji hukumomin gidan yarin a ranar Lahadi.
An sake kama bakwai daga cikin fursunonin da suka tsere a wani samame da jami’an tsaro suka gudanar, kamar yadda Umar Abubakar, mai magana da yawun hukumar gidan yari ta Nijeriya ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar.
“Ambaliyar ta rusa katangar gidajen gyara halin da suka hada da Cibiyar Kula da Matsakaicin Tsaro, da ta rukunin gidajen ma’aikatanta da ke cikin birnin,” in ji Abubakar.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan nemo da mayar da sauran fursunonin.
Mummunar ambaliya a shekaru 30
Maiduguri babban birnin jihar Borno, ya fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru da dama, a farkon makon da ya gabata.
Ambaliyar ta fara ne a lokacin da wata madatsar ruwa ta cika bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, lamarin da ya lalata gidan namun dajin na jihar tare da kora kadoji da macizai a cikin al'ummomin da ambaliyar ta mamaye.
Ambaliyar ta kashe akalla mutum 30 a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar, sannan ta shafi wasu miliyan guda, tare da tilasta wa dubban mutane komawa sansanonin ‘yan gudun hijira.