Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun jagoranci ƙulla yarjeniyoyi daban-daban tsakanin ƙasashen biyu ranar Lahadi a birnin Doha.
Ƙasashen biyu sun sanya hannu kan jarjeniyoyin da suka shafi harkokin "ilimi da zuba jari da inganta rayuwar matasa da harkokin ma'adinai da harkokin yawon buɗe ido da wasanni," in ji wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban Nijeriya ya fitar.
Gabanin bikin sanya hannu kan yarjeniyoyin a Fadar Shugaban Ƙasar Qatar, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa mai masaukin baƙi cewa a shirye gwamnatinsa take ta yi maraba da masu zuba jari a ƙasar, yana mai yin nuni da sauye-sauyen da yake gudanarwa waɗanda za su taimaka wurin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da samun tagomashi a harkar zuba jari da kyautata al'adu.
"Babban jarinmu shi ne al'umarmu. Ƙarfinmu ya ta'allaƙa kan ƙwazon matasan Nijeriya. Suna da kuzari da basira da jajircewa. Za su kasance abokan hulɗa a masana'antun Qatar. Suna da ilimi da nagarta, kuma suna neman inganta kowane tsari da suka samu," a cewar Shugaba Tinubu.
Shugaban na Nijeriya ya jinjina wa gwamnatin Qatar bisa sauye-sauye da ci-gaban da take samu, yana mai cewa babban burinsa shi ne Nijeriya ta samu irin wannan tagomashi.
"Mun gani ƙarara yadda Qatar ta samu ci-gaba cikin sauri. Ba zai yiwu mutum ya kawar da kai daga irin wannan nasara da kuka samu ba. Shugabannin wannan ƙasa sun yi abin da ya dace, kuma mu ma mun zo nan ne domin mu yi koyi da ku," a cewar Shugaba Tinubu.
A nasa ɓangaren, Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya jaddada cewa a shirye ƙasarsa take ta yi maraba da batun zuba jari da Shugaba Tinubu ya gabatar, yana mai cewa ya je Nijeriya a 2019 saboda muhimmancinta a harkokin ci-gaban duniya.
"Ba ni da shakku game da jajircewar al'ummar Nijeriya. Duk duniya ta san irin ƙwazonsu da aiki tuƙuru. Abin da ya rage kawai shi ne mu ga sun aiwatar da hakan a cikin Nijeriya ba a wajenta ba," in ji shi.
Nan-take Shugaba Tinubu ya wakilta Ministan Harkokin Kuɗi, Mr. Wale Edun a matsayin jagoran tawagar gwamnati Nijeriya wadda za ta tattauna da ɓangaren Qatar kan tsarin zuba jari da yadda za a aiwatar da shi.
Kazalika shugaban Nijeriya ya umarci Ministan Ma'adinai Dele Alake da ya gabatar da taƙaitaccen bayani game da ɗimbin ma'adinai da ake da su a ƙasar, ciki har da ma'adinin lithium.
Daga nan ne kuma ƙasashen suka sanya hannu kan yarjeniyoyi bakwai a fannin ilimi; tsarin gwamnatin Qatar na ɗaukar ma'aikata; haɗin-gwiwa don kafa majalisar kasuwanci (JBC) tsakanin cibiyar kasuwanci ta Qatar da takwararta ta Nijeriya, Ma'adanai, da aikin gona; baya ga yarjejeniya kan matasa da wasanni.