Mr Egbetokun, wanda wani babban jami’in ƴan sanda AIG Ben Okolo ya wakilce shi a taron, ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai haifar da rikicin ƙabilancin da jawo rarrabuwar kawuna a jihohin ƙasar. Hoto: NGP

Sufeto-Janar na rundunar ƴan sandan Nijeriya ya yi watsi da batun shirin samar da rundunar ƴan sandan jihohi, yana mai cewa ƙasar ba ta kai matsayin da za ta iya samar da wannan tsari ba.

Kayode Egbetokun ya bayyana matsayarsa ne a ranar Litinin a wajen wani taro da ake tattaunawa a kan samar da rundunonin ƴan sandan jihohi da Majalisar Wakilan Kasar ta shirya a Abuja.

Mr Egbetokun, wanda wani babban jami’in ƴan sanda AIG Ben Okolo ya wakilce shi a taron, ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai haifar da rikicin ƙabilancin da jawo rarrabuwar kawuna a jihohin ƙasar.

"Matsayar shugabancin rundunar 'yan sandan Nijeriya ita ce har yanzu Nijeriya ba ta shiryawa kuma ba ta yi ƙarfin kafa rundunar 'yan sandan da ke ƙarƙashin ikon jihohi ba," in ji shi.

Wannan kalamai na Sufeto-Janar na ƴan sanda na zuwa ne watanni biyu bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamiti da zai yi duba game da yiwuwar kafa rundunar ƴan sandan jihohi, a wani yunƙuri na magance matsalolin tsaro masu tasowa.

"Matsayata a bayyane take. Dole mu yi da karfinmu domin mu binciki batutuwan da ke akwai ciki har da yiwuwar kafa rundunar ƴan-sanda mallakar jihohi," kamar yadda shugaban ya bayyana wa ƴan Nijeriya, yana mai bayyana dalilin matakin.

Sufeto-Janar na rundunar ‘yan sandan ya ce kafa ‘yan sandan jihohin zai kuma haifar da tsarin kwamandoji da yawa a jihohin.

Ya kuma ce akwai yiwuwar gwamnonin jihohi su yi amfani da damar rundunonin ‘yan sandan jihar ta hanyar amfani da su wajen cimma wata manufa ta siyasa, wanda hakan zai haifar da cin zarafin bil’adama.

Maimakon kafa rundunar ‘yan sandan jihar, ya ba da shawarar a haɗe jami’an tsaro da na Civil Defence da kuma hukumar kiyaye hadurra ta tarayya domin kafa sashe a rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Ya kuma ce akwai bukatar daukar jami’an ‘yan sanda kusan 30,000 aikin a duk shekara domin cimma muradun Majalisar Dinkin Duniya na aikin ‘yan sanda, tare da kara yawan kasafin kudin shekara ga rundunar.

TRT Afrika