Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta naɗa sabbin ministocin ma'adinai da makamashi a wani garambawul da ta yi . Hoto: Fadar Shugaban Nijar na X

Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta naɗa sabbin ministocin ma'adinai da makamashi a wani garambawul da ta yi, inda ta raba ma'aikatar ma'adinai da man fetur da makamashi zuwa gida uku, kamar yadda ta sanar a ranar Litinin

Tsohon ministan ma'adinai da man fetu da makamashi Mahaman Moustapha Barke Bako shi ne ministan man fetur a yanzu.

Sai Farfesa Amadou Haoua da aka naɗa sabon ministan makamashi da kuma Kanal Ousmane Abarchi a matsayain ministan ma'adinai, kamar yadda wata dokar ƙasa ta tsara da aka sanar a gidan talabijin na ƙasar, wacce ba ta bayyana dalilin yin garanbawul din ba.

Duk ma'aikatun uku suna da matuƙar muhimmanci ga ƙsar ta Yammacin Afirka, inda jami'an soji ke mulkinta bayan kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya a watan Yuli.

Nijar na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da ma'adinin yuraniyom, wanda ake amfani da shi a faɗin duniya wajen samar da makamashin nukiliya.

Ƙasar na fatan bunƙasa samanr da man fetur ɗinta zuwa ganga 110,000 a dk rana daga kusan ganga 20,000 da tkae samarwa ta hanyar sabon bututunta na Nijar zuwa Jamhuriyar Benin, wanda aka ƙaddamar a bara.

Reuters