Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kulla sabuwar yarjejeniya da kamfanin Orano Mining na kasar Faransa don hakar ma’adanin uranium.
Ministar ma’adanai ta kasar, Hadizatou Ousseini Yacouba, da takwaranta na Ma'aikatar Kudi, Ahmat Jidoud ne suka wakilci kasar ranar yayin kulla yarjejeniyar a Yamai ranar Aalhamis.
Shugaban kamfanin Orano, Nicolas Maes, shi ya jagoranci tawagar kamfanin makamashin.
Bangarorin biyu sun amince a tsawaita yarjejeniyar hakar uranium a kasar zuwa shekarar 2040.
Kamfanin Orano, mai aikin hakar uranium a kasashen Canada da Kazakhstan da Nijar, ya bayyana cewa wannan sabuwar yarjejeniya wata shaida ce ta kokarin jaddada alaka mai dorewa tsakaninsu.
Orano ne ya maye gurbin kamfanin Areva, wanda ya yi aikin hakar uranium na kusan shekaru 50 a Jamhuriyar Nijar, inda ya hako makamashin da yawanci ake kai wa Faransa.
Kamfanin Orano Mining ya hako tan 140,000 na makamashin uranium zuwa yanzu, daga soma aikinsa.
'Sahun gaba'
Nijar daya ce daga cikin manyan kasashe masu arzikin uranium, wanda ake amfani da shi wajen samar da lantarki da fasahar nukiliya, da kuma kera makamin nukiliya.
Ga kasar Nijar, wannan hadin-gwiwa ya tabo ka’idojin cigaba da aiki a mahakar Somaïr, da gyara muhalli a filin hakar ma’adanai na Cominak wanda aka rufe a 2021, da kuma kudurin Orana na tallafa wa jama’ar Nijar.
Yarjejeniyar za ta mai da hankali kan bukatar Nijar ta cin moriyar arziki da samun kudin shiga daga kamfanonin da ke hakar ma’adanai a kasar.
Akwai batun kare muhalli, musamman alkinta arzikin yankin Somaïr wanda zai ci gaba da aiki har nan da shekara 11, da takaita tasirin rufe tashar hakar uranium ta Cominak.
Shirin mahakar Imouraren
Game da shirin Imouraren kuwa, kasar Nijar ta amince da kamfanin Orano zai bi diddigin nemo zabin hakar uranium a yankin Imouraren na jihar Agadez.
Bangarorin biyu sun amince da jinkirta fara hakar ma’adanai a mahakar Imouraren, wadda take da kimanin uranium tan 200,000.
A baya an shirya fara aiki a shekarar 2015, amma sai aka dakatar lokacin da farashi uranium ya karye bayan hatsarin tashar nukiliya ta Fukushima da ke Japan a shekarar 2011.
An ware Euro miliyan 85 don zuba jari a shirin fayyace dabarun soma aiki a Imouraren, don kokari a fannin kimar muhalli a yankin, ta la’akari da fasaha, muhalli da tattalin arziki.
Ana sa ran kai wa matakin yanke hukunci kan zuba jari zuwa shekarar 2028, bayan an kammala aikin tantance dacewar aiki a yankin.
Ma’aikatun gwamnatin Nijar daban-daban ne za su sa ido kan wannan shiri, tare da hadin gwiwar al’ummomi mazauna yankin, don rage mummunan tasirin da hakar ma'adanai ka iya haifarwa
Tsarin tallafa wa jama’a
An zabi duba bangarori uku don taimakon jama’a: inganta kwarewar aikin ma'aikata, da ilimin ‘ya’ya mata kamar gina makarantun kwana, da kawo cigaban tattalin ariziki a samar da makamashi.
Za a aiwatar da wadannan shirye-shirye da za su lashe Euro miliyan 40 zuwa 2030.