Abdourahamane Tiani ya karbi mulki ne a ranar 26 ga Yulin 2023 bayan hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum. / Photo: AFP

Jamhuriyar Nijar na kan wata turba ta zama ƙasa mai cikakken 'yanci, in ji shugaban sojojin kasar a wani jawabi da ya yi a ranar Alhamis na bikin cika shekara daya da juyin mulkin da ya kai shi karagar mulki.

Abdourahamane Tiani ya karbi mulki ne a ranar 26 ga Yulin 2023 bayan hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Tiani ya ce, "Tafiyar mu zuwa ga cikakken 'yancin cin gashin kai ba abu ne da ba mai iya hana mu kai wa ga ci," in ji Tiani, kwanaki biyu bayan da ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka Faransa ta bukaci a gaggauta sakin Bazoum daga tsare shi ba tare da wani sharadi ba.

Tiani ya kara da cewa, "Babu wata jiha, ko wata kungiya mai zaman kanta da za ta gaya mana yadda za mu yi, ko kuma ta sa na gaya mata wane shiri nake yi na kulla ƙawance ko diflomasiyya."

Faransa ta yi Allah wadai da tsare Bazoum bayan yanke shawarar ɗage kariyar da yake da ita da har aka yi amfani da hakan wajen gurfanar da shi.

Tiani shi ne shugaban masu gadin Fadar Shugaban Ƙasa na Bazoum kafin ya sauke shi daga mulki.

Tiani ya ce, "Wadanda ke tunanin komawar kan karagar mulki za su ji kunya," in ji Tiani, yana mai jaddada cewa kasar Afirka ta Yamma na kan hanyar "karya tsarin mulkin mallaka".

Tun bayan juyin mulkin ne gwamnatin mulkin sojan kasar ta fara nisanta kanta da kasar Faransa, ta kuma kafa sabon ƙawance da kasar Rasha.

Nijar ta sha fama da takunkumai daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS saboda juyin mulkin da ta yi, lamarin da daga farko-farko ya jijjiga ta, musamman na katswar alaƙa da manyan maƙwabtanta Nijeriya da Benin.

Amma samun goyon bayan Mali da Burkina Faso da ta yi, waɗanda su ma ke ƙarƙashin mulkin soja, ya sa ta ji wani ƙrfi na tunkarar duk ƙalubalen da ke gabanta, a cewar masu sharhi.

An yi ta samun takun-saƙa tsakanin ECOWAS ta bakin shugabanta wato Bola Tinubu na Nijeriya da gwamnatin mulkin sojin Nijar, lamarin da ya sa har sai da masu ruwa da tsaki na yankin da dama suka dinga saka baki.

Daga baya ECOWAS ta janye takunkuman, amma Nijar tuni ta yanke shawarar ficewa daga ƙungiyar tare d ahaɗa kai da Mali da Burkina Faso suka kafa wata sabuwa ta Ƙawancen Ƙasashen Yankin Sahel.

TRT Afrika da abokan hulda