Gwamnatin Nijar ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya jawo ambaliya ya sanya an jinkirta fara sabuwar shekarar karatu da kusan wata guda.

Gwamnatin Nijar ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya jawo ambaliya ya sanya an jinkirta fara sabuwar shekarar karatu da kusan wata guda.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya addabi mafi yawan al'ummar yammacin Afirka tun cikin watan Yuni, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da shafar dubban daruruwan mutane.

Kasar ta yankin Sahel da sojoji ke jagoranta na daga cikin yankunan tsakiya da yammacin Afirka da ke fama da ambaliyar ruwa a daidai lokacin da ake samun ruwan sama da ba a saba gani ba.

Gwamnati ta sanar da cewa ta mayar da ranar farko ta makaranta - wadda aka tsara a ranar 2 ga Oktoba - zuwa ranar 28 ga Oktoba ga kusan daliban kasar miliyan 4.5.

'Lamarin ya shafi makarantu'

"Lamarin ya shafi makarantu da dama, wasu kuma wadanda abin ya shafa ruwa ya mamaye su," in ji wata sanarwar gwamnati da aka karanta a gidan talabijin na kasar a yammacin ranar Alhamis.

A tsakiyar Maradi da ke kudancin kasar, yankin da rikicin ya fi kamari, an kafa tantuna 100 domin daukar mutane a makarantu.

Bisa kididdigar da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fitar daga ranar 4 ga watan Satumba, mutane 273 ne suka mutu, 121 daga cikinsu sun nutse yayin da 152 suka mutu sakamakon rugujewar gidaje.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya shafi mutane sama da 700,000, kamar yadda hukumomi suka bayyana a farkon wannan wata.

Fiye da tan 9,700 na hatsi ne aka samar a wannan watan ga mutanen da ke zaune a yankuna takwas da ambaliyar ruwa ta shafa, ta kara da cewa "an shawo kan lamarin".

Masallaci mai tsohon tarihi ya rushe

Wani mashahurin masallacin tsakiyar karni na 19 da aka yi da kasa da bambaro a birni na biyu mafi girma a Jamhuriyar Nijar, Zinder, ya ruguje sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a farkon watan nan.

An kuma nuna damuwa a arewacin birnin Agadez, da ake kira hanyar shiga hamada, game da barnar da ambaliya ta yi a cibiyarta mai dimbin tarihi, wurin tarihi na UNESCO.

A bisa ka'ida daga watan Yuni zuwa Satumba, daminar Nijar kan jawo asarar rayuka, inda a shekarar 2022 mutane 195 ne suka mutu.

Masana kimiyya sun dade suna gargadin cewa sauyin yanayi da hayaki mai gurbata muhalli ke haifar da matsanancin yanayi kamar ambaliyar ruwa da yawa, mai tsanani da kuma daɗewa.

AFP