Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ba zai fahimci cewa ya yi asara ba sai nan gaba.
Ya bayyana haka ne jim kadan bayan Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen gwamnan jihar Kano.
Tun can dama akwai ‘yar tsama tsakanin Ganduje da tsohon mai gidansa Kwankwaso inda suka dade da raba gari.
Sai dai a tattaunawarsa da TRT Afrika, Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa yanzu za su mayar da hankali wajen yin aiki gadan-gadan domin ci-gaban al’ummar Jihar Kano.
Ya ce Abdullahi Umar Ganduje ne babban wanda ya tafka asara a shari’ar da Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar wa Abba Kabir Yusuf mukaminsa na gwamnan Kano.
“Ba ni da wani labari ko wani sako. Ai mai girma tsohon shugaban kasa ya ce jiki magayi. Duk abin da za ka yi ka zama mai daraja. Kada ka yarda ka zubar da mutuncinka kamar yadda suka zubar da mutunci,” in ji Kwankwaso.
“Ka ga mutunci madara ne idan ya riga ya zube shikenan ya lalace. Na tabbata shi (Ganduje) shi ya fi kowa asara domin ba zai gane asarar ba sai nan gaba kadan. Daga shi sai wanda ya yi takarar gwamna Gawuna,” in ji Kwankwaso.
“Ya dauki layi na mutunci da daraja ya yarda bai ci zabe ba. Amma zama da madauka kanwa suka je suka zuga shi ya zo ya dauka cewa ga wata banza ta fadi kawai zai ci banza shi ma kamar yadda mai gidansa ya ci banza a shekara ta 2019.
“Wannan duka darasi ne. Kowanne daga cikinsu da mu da muke wannan bangare na NNPP ko Kwankwasiyya da jama’ar jihar Kano da Nijeriya har ma shi da kansa shugaban kasa da ya fi samun kwanciyar hankali da ba su kai karar nan ba.
“Amma mafi muhimmanci a wurinmu mu da ba sa sonmu yanzu sun yi wani abu da ya jawo wanda ake cewa tun da aka yi jihar Kano a sanin masana da masu shekaru ba a taba yin abubuwa da aka yi addu’a a Kano da kasar nan da kasashen duniya kamar wannan ba,” kamar yadda Kwankwaso ya kara da cewa.
Abin da muka sa a gaba
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta NNPP halin yanzu za ta mayar da hankali domin yi wa al'ummar jihar Kano ayyuka.
"Mu dama a tsarinmu tsari ne na harkar ilimi. Harkar ilimin nan a nan aka sanmu da ita kuma ita ce karfinmu. Na tabbata ita ce ta fi dukkanin abubuwa da za ka iya tunani na harkar gwamnati," in ji Kwankwaso.
"Amma yanzu da yake harkar tsaro ta shigo, ko yau din nan mun yi magana da mai girma gwamna ya gaya mini irin abubuwan da yake so ya yi na tsare-tsare wanda za a kawo a jihar Kano.
"Idan Allah ya yarda gwamnatin Kano za ta dauki mataki na kare al’ummarta a zauna lafiya a yi ilimi a yi noma a yi sana’o’i da sauransu domin kasa ko jiha ta ci gaba. Idan Allah ya yarda sai Kano ta zama jihar misali daga nan zuwa shekara hudun nan ko uku da suka rage na wannan mulki," kamar yadda Sanata Kwankwaso ya kara da cewa.