Hukumar NAFDAC wadda ke kula da ingancin abinci da magunguna ta buƙaci a fara yanke hukuncin kisa ga waɗanda ke safarar jabun magunguna.
Daraktar hukumar Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka inda ta ce ya kamata a ɗauki wannan mataki musamman sakamakon yadda irin waɗannan magungunan ke jawo mutuwar yara, kamar yadda ta shaida wa gidan talabijin na Channels a ƙasar.
“Wani ya sayi magungunan yara kan N13,000, wani kuma yana sayar da shi N3,000 a cikin rukunin shaguna ɗaya,” kamar yadda shugabar ta NAFDAC ta bayyana a ranar Juma’a.
Shugabar ta NAFDAC ta bayyana cewa babu wasu sinadaren magance cuta da aka gani a cikin maganin bayan an gudanar da gwaji a kan maganin a ɗaya daga cikin ɗakunan gwajin na hukumar da ke Kaduna.
Hukumar ta NAFDAC ta bayyana cewa tana neman a samu goyon bayan ɓangaren shari’a domin su bayar da goyon baya kan hakan.
Ta bayyana cewa hukumar na aiki tare da ‘yan majalisa domin ganin haƙarsu ta cim ma ruwa.