Nijeriya ta yi asarar aƙalla dala biliyan uku a satar ɗanyen man fetur daga watan Janairun 2021 zuwa Fabrairun 2022. Hoto: Reuters

Fashewar wani abu da tashin wuta a wata haramtacciyar matatar man fetur a yankin Neja-Delta a Nijeriya sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 15 ciki har da wata mace mai ciki, kamar yadda mazauna yankin da ƙungiyoyin rajin kare muhalli suka faɗa a ranar Talata.

Fashewar ta faru ne a ranar Litinin a gundumar Emohua da ke Jihar Ribas, inda amfani da haramtattun matatun mai ya zama kamar ruwan dare.

Mazauna yankin sun ce akwai yiwuwar yawan waɗanda suka mutun zai ƙaru saboda mafi yawancin mutanen sun ƙone ƙurmus, sannan wasu gommai kuma sun ji munanan raunuka.

Ƴan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin amma ba su bayar da cikakkun bayanai na yadda abun ya faru ba. Mazauna yankin sun ce mafi yawan mutanen da suka mutun suna aiki ne a haramtacciyar matatar man da ke ƙauyen Rumucholu.

Fasa bututu

Mutanen da ke aiki a wajen na tace fetur din da suka kwasa ne daga bututun da aka fasa, in ji Chima Avadi, wani mai fafutuka a yankin. "Idan suka kwashi fetur din daga wajen da suka fasa bututun, sai su kai inda suke girki su ajiye. Ta haka ne wuta ta tashi a wajen," in ji Avadi.

Ya ce a yanzu haka an kwantar da gomman mutane a asibitoci. Cikin mutum 15 ɗin da suka mutu har da wata mace mai ciki, a cewar wata sanarwar da Cibiyar Ci gaban Matasa da Muhalli ta faɗa.

Ana yawan samun fashewar abubuwa a haramtattun matataun fetur ɗin da suka zama ruwan dare a yankin Neja-Delta, inda a can ne manyan cibiyoyin arzikin fetur na Nijeriya suke, waɗanda masu satar mai ke yawan hara.

Mutane da dama na kafa haramtattun matatun mai a yankunan da suke cikin surƙuƙi.

Samun makuɗan kuɗaɗe

Mutanen da ke aiki a irin waɗannan wuraren ba sa bin dokoki da ƙa'idoji, lamarin da ya sa ake yawan samun gobara, ciki har da wacce ta taɓa kashe fiye da mutum 100 a Jihar Imo a bara.

"Kudin da suke samu a cikin kwana ɗaya ya fi abin da wani ma'aikacin gwamnatin ke samu a shekara ɗaya," in ji shugaban ƙungiyar ci gaban matasa da kula da muhallin, Fyneface Dumnamene.

Ƙungiyarsa tana ƙoƙarin ganin an samar da sauye-sauye a fannin muhalli don kawo ƙarshen haramtattun ayyuka.

Amma a yayin da ake fama da matsalolin tattalin arziki a Nijeriya, "mutane na neman damarmakin za su samu kuɗi don su rayu," in ji Dumnamene.

An yi asarar dala biliyan uku na ɗanyen man fetur

Nijeriya ta yi asarar dala biliyan uku daga satar ɗanyen man fetur daga tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Fabrairun 2022, kamar yadda Kamfanin Man Fetur na ƙasar ya faɗa a bara.

A matsayinta na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka da suke samar da arzikin man fetur, Nijeriya na samun mafi yawan arzikinta ne daga yankin Neja-Delta.

Haka kuma mazauna yankin na cewa al'ummominsu ba sa samun ababen more rayuwa kuma suna ganin kamar gwamnati ta yi watsi da su.

AP