A yanzu mutane da dama da suka rasa muhallansu suna samun mafaka a sansanoni. / Hoto: Reuters 

Wata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Nijeriya ta bayyana cewa, ana fama da matsalar jinƙai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, bayan da mummunar ambaliyar ruwa ta raba mutane sama da miliyan guda da muhallansu tare da gajiyar da ma’aikatan lafiya.

Yankin da tuni yake fama da matsalar ta da ƙayar bayan da aka dade ana fama da shi, yanzu haka yana fuskantar yiwuwar bullar cututtuka masu yaduwa ta ruwa.

Ambaliyar ruwan wadda ita ce mafi muni cikin shekaru 30 da suka gabata, ta yi sanadin mutuwar mutum fiye da 30.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway NRC ta bayyana cewa, a karshen mako, an samu karin mutum 50,000 da suka rasa matsugunansu a arewa maso gabashin Nijeriyar, yayin da ambaliyar ruwa ta tsananta.

Ƙaruwa tsananin buƙata

"Halin da ake ciki a yankin Sahel da Tafkin Chadi yana kara ta'azzara, saboda illar tashe-tashen hankula, da matsugunai, da sauyin yanayi na yin illa ga masu rauni," in ji Hassane Hamadou, daraktan yankin tsakiya da yammacin Afirka ta NRC.

Yawancin mutanen da suka rasa matsugunansu suna zaune ne a sansanoni ba tare da samun abinci ko tsaftataccen ruwan sha ba, lamarin da ya sa suke fama da rashin lafiya musamman.

Lamarin dai ya kara ta'azzara ne sakamakon matsin da hukumomin agaji da albarkatun gwamnati ke fuskanta.

Ambaliyar ruwa a Borno, cibiyar Boko Haram, ya samo asali ne sakamakon wani dam da ya ɓalle bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

Ambaliyar ruwa a yankin Sahel

Irin wannan ambaliya ta afku a wasu sassan yankin Sahel da suka hada da Kamaru, Chadi, Mali, da Nijar.

A cikin makonni biyu da suka gabata, ambaliyar ruwa a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka ta yi sanadiyar raba mutane sama da miliyan 1.5 da muhallansu tare da haddasa mutuwar kusan 465 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A arewa maso gabashin Nijeriya kadai, an samu karin mutane 50,000 da suka rasa matsugunansu a 'yan kwanakin nan.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norway NRC, ta yi gargadi game da mummunan halin da ake ciki a yankin, inda ta bayyana illolin da tashe-tashen hankula, da raba mutane da matsugunansu, da sauyin yanayi ke haifarwa ga jama'a masu rauni.

An yi wa fannin lafiya yawa

A Maiduguri, babban birnin jihar Borno, daruruwan mutane na dakon ganin likitoci, saboda da dama daga cikinsu na fama da cututtuka kamar gudawa. Bintu Amadu, wacce danta ba shi da lafiya, ta bayyana takaicinta na neman magani ba tare da samun nasara ba.

Ramatu Yajubu, duk da cewa an ba ta lokacin ganin likita, ta shiga rashin tabbas game da ganin nasa, saboda yadda mutane suka yi yawa.

Mathias Goemaere na kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ya jaddada karuwar hadarin kamuwa da cututtuka na ruwa a tsakanin al'ummar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki da rarraunan tsarin rigakafi.

Gwamnatin Nijeriya ta fitar da wani gargadi game da karuwar ruwa a kogin Benuwai da Neja, lamarin da ka iya janyo ambaliya a yankin kudancin Neja Delta.

TRT Afrika