Bayanai sun nuna cewa matakin da lafari ya ɗauka ne bai wa 'yan wasa biyu na Labe jan kati tare da bugun fenareti shi ne ya jawo rikicin..Hoto:OTHER

Mutane fiye da 100 sun mutu yayin da gommai suka jikkata bayan wani rikici ya ɓarke ranar Lahadi yayin gasar ƙwallon ƙafa a kudu maso gabashin ƙasar Guinea.

Rikicin ya ɓarke ne bayan magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Labe sun ƙi amincewa da ƙwallon da ƙungiyar Nzerekore ta zura musu, lamarin da ya kai ga taho-mu-gama a Nzerekore, birni na biyu mafi girma a ƙasar, wanda ke da nisan kilomita kusan 570 daga Conakry, babban birnin ƙasar, a cewar jaridar Mediaguinee.

Bayanai sun nuna cewa matakin da lafari ya ɗauka ne bai wa 'yan wasa biyu na Labe jan kati tare da bugun fenareti shi ne ya jawo rikicin.

“Rikicin ya ɓarke ne yayin da magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafar suka riƙa jifa da duwatsu a cikin filin wasa. Jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin kwantar da rikicin ta hanyar fesa tiyagas, sai kawai komai ya hargitse a cikin filin wasan inda aka yi ta ba-ta-kashi,” in ji jaridar.

Ko da yake kawo yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba, amma majiyoyi daga asibiti sun ce "gommai ne suka riga mu gidan gaskiya." Wani likita ya ce mutanen da suka mutu za su "kai 100."

Firaministan Guinea Bah Oury ya yi Allah wadarai da aukuwar rikicin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

“Gwamnati tana nuna takaici game da rikicin da ya ɓarke yayin wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Labe da ta Nzerekore a Nzerekore," in ji shi.

"Gwamnati tana bibiyar lamarin hau da ƙafa kuma tana jaddada kira da a zauna lafiya domin bai wa asibitoci damar kula da mutanen da suke buƙatar taimako.”

Wasan da ake bugawa shi ne na ƙarshe a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa da Shugaban ƙasar Guinea Janar Mamady Doumbouya ke ɗaukar nauyi.

AA