Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce suna fatan Allah zai bai wa sabon gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf hikimar warware matsalolin da aka shuka a jihar.
Ya bayyana haka ne yayin da yake karin haske kan jita-jitar da ake yadawa cewa idan sabon gwamnan, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya karbi ragamar mulkin Kano zai mayar da tsohon sarki Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarauta.
Kwankwason ya yi bayani ne a hira da wani gidan talabijin a ziyarar da ya kai kasar Kamaru.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023 ya ce akwai bukatar sake nazari game da yadda aka rarraba masarautun jihar.
“Mun yi kokari ba mu sanar da maganar sarki - ko za a cire ko za a sa ko za a yi kaza ba, amma yanzu ka ga dama ta samu, su wadanda Allah ya bai wa wannan ragama su za su zauna... Za su je su duba su gani mene ne ya kamata su yi a halin da suka samu kansu,” kamar yadda tsohon sanatan a Nijeriya ya bayyana.
Ya kuma tabo batun rarraba Masarautar Kano da gwamnatin mutumin da ya gaje shi Abdullahi Umar Ganduje ta yi inda ya ce akwai bukatar a sake nazari.
“Ita sarautar yanzu an kasa ta kashi biyar, duka wadannan da aka yi dole sai an zo an yi nazari,” in ji shi.
Ya bayyana cewa kowane shugaba tun daga kan na kasa zuwa na karamar hukuma idan ya zo yakan gaji abubuwa masu kyau da masu wahalar warwarewa.
“Mun tabbatar shi wannan gwamna Allah zai ba shi hikima da basira na yadda zai zo ya warware wadannan matsaloli da aka zo aka shuka a Jihar Kano,” in ji Kwankwaso.
Ya kara da cewa a matsayinsa na dattijo "za mu ci gaba da ba su shawarwari, yadda za su yi abin da ya dace."