Gwamnatin Jihar Kogi da ke yankin tsakiyar Nijeriya ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ceto wasu ɗaliban Jami’ar Confluence ta Kimiyya da Fasaha da 'yan bindiga suka sace a ranar Alhamis da daddare.
Sanarwar da Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa na jihar Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Juma’a ta ce “samun labarin harin ke da wuya sai Mai girma Gwamna Alhaji Ahmed Usman Ododo ya yi maza ya tsara matakan tsaro don bin sawun masu garkuwa da mutanen tare da tabbatar da an kuɓutar da daliban da aka sace da kuma kama maharan.”
Gwamnatin ta ce an tura ɗaruruwan mafarauta da suka san lungu da saƙo na yankin tare da jami’an tsaro don ceto ɗaliban, waɗanda aka sace a yayin da suke aji suna ɗaukar darasi.
Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa ɗalibai tara aka sace.
“Muna son tabbatar wa ɗalibai da iyaye da duka al’ummar Jihar Kogi cewa gwamnati na tsaye tsayin daka a kan lamarin, kuma za a ceto ɗaliban da ransu da lafiyarsu.
"Gwamna Usman Ododo ya kuma umarci jami’an tsaro da su zagaye dukkan makarantun jihar don ba su tsaro.”
Yadda abin ya kasance
A ranar Alhamis da daddare ne ‘yan bindiga suka kai hari Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence (CUSTEC) da ke garin Okene, inda suka yi awon-gaba da wasu ɗalibai.
Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki jami’ar ne da misalin karfe 9:00 na dare yayin da daliban ke karatun jarabawar da za su fara ranar Litinin 13 ga watan Mayu, kamar yadda Jaridar DailyTrust ta ruwaito.
Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun shiga makarantar ne ta cikin daji, suka shiga dakunan karatu uku, suka fara harbin iska. “Sun kama daliban a cikin ajin, suka fara daukar su; makarantar ta shiga cikin rudani, yayin da daliban da suka firgita a wasu ajujuwan suka yi ta tururuwa, suna tururuwa ta bangarori daban-daban.
“Ko kafin jami’an tsaro na makarantar da na waje far farga, tuni ‘yan bindigar sun yi nasarar sace wasu dalibai. Amma kokarinsu ya rage girman ɓarnar da aka yi saboda maharan ba su wuce dakunan ajujuwan farko guda uku ba,” in ji majiyar.