Hedkwatar tsaron ta ce an kashe kwamandojin 'yan ta'adda dama a cikin watan na Agusta.  / Hoto: Reuters

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta sanar da cewa dakarun sojin ƙasar sun kashe ‘yan ta’adda 1,166, sannan sun kuma kama mutane 1,096 da ake zargi da ayyikan ta'addaci a watan nan na Agusta.

Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Alhamis, kuma aka watsa shi kai-tsaye ta shafin Facebook na rundunar.

Janar Edward ya kuma ƙara da cewa dakarunsu sun kuɓutar da mutane 721 da aka yi garkuwa da su a cikin watan na Agusta.

Ya ce an kuma ƙwato makamai da dama da suka haɗa da bindigogi 391 da albarusai 15,234 sannan an ƙwato kayayyaki da kuɗinsa ya haura naira biliyan biyar.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kashe da waɗanda aka kama, akwai manyan kwamandojin ‘yan ta’adda musamman a yankin arewa maso yamma.

“Alal misali, a rewa masu gabas a cikin wannan watan na Agusta kawai mun kashe waɗannan jagororin ‘yan ta’addar da kwamandoji, Munir Arika da Sani Dilla (wanda aka fi sani da Dan Hausawan Jibilarram), da Ameer Modu da Dan Fulani Fari Fari, da Bakoura Araina Chikin, Dungusu da Abu Darda da kuma Abu Rijab” a cewar Janar Edward.

Ya ce a can ma shiyyar arewa maso yamma sojojin na Nijeriya sun samu nasarar kashe wasu gaggan ‘yan fashin daji da ‘yan ta’adda da suka addabi yankin.

Ya ce cikin waɗanda aka kashe a shiyyar sun haɗa da “Kachalla Dan Ali Garin Fadama da Kachalla Dan Mani Na Inna da Kachalla Basiru Zakariyya, da Sani Bakatsine da Inusa Zangon Kuzi.”

Sauran wuraren da Janar Edward ya ce sun yi aiki sun kuma samu nasar sun haɗa da shiyyar kudu maso gabashin kasar da kuma shiyyar kudu masu kudu.

TRT Afrika