Yaƙin Sudan ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu. / Hoto: AFP

Manyan jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun gargaɗi Kwamitin Tsaro na majalisar kan haɗarin samuwar sabon fagen daga a Sudan, a wajen garin el-Fashe da ke Darfur, a yankin da al'umma ke dab da faɗawa matsalar yunwa.

Shekara guda kenan ana gwabza yaƙi, tsakanin rundunar sojin Sudan, SAF ƙarƙashin Janar Abdel Fattah al Burhan, da rundunar ɗaukin gaggawa ta ƙasar, RSF ƙarƙashin Janar Mohamed Hamdan Dagalo.

Rosemary DiCarlo, ƙaramar sakatariya kan siyasa da zaman lafiya a Majalisar Ɗinkin Duniya, ta faɗa ranar Juma'a cewa, ƙasar na fama da "rikicin da ba za a iya kwatantawa ba... wanda ɗan'adam ne ya janyo shi".

DiCarlo ta ce, "Rundunonin da ke yaƙar junansu sun yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta... a maimakon haka, suna iza wutar ci gaba da yaƙin, inda rundunonin na SAF da na RSF suke ci gaba da shigar da farar-hula aikin soji".

Ta ambata damuwarta kan rahotannin tsoron aukuwar wani hari da "ke tafe" daga rundunar RSF, kan garin el-Fasher, wanda shi ne babban birni ɗaya cikin jihohi biyar na yankin Darfur wanda ba ya ƙarƙashin ikonta, "wanda haka ke barazanar samuwar sabon fagen-daga a rikicin."

El-Fasher shi ne garin da ya zama sansanin ayyukan jinƙai ga Darfur, wanda yake ƙunshe da kusan rabin-rabin al'ummar Sudan miliyan 48.

'Ƙazamin faɗan ƙabilanci'

Kafin kwanan nan, garin el-Fasher ya kasance wanda faɗa bai shafa ba, inda tarin 'yan gudun hijira suka samu matsuguni.

Amma tun tsakiyar Afrilu, an samu rahotannin fashe-fashen bama-bamai da karon-batta a ƙauyukan da ke gefen garin.

Edem Wosornu, darakar ofishin MDD kan Daidaita Batutuwan Jinƙai, ta yi nuni da cewa ƙungiyar Doctors Without Borders ta yi wa waɗanda aka jikkata su sama da 100 aiki a 'yan kwanakin nan.

Ta ce, "Tun lokacin nan, an yi ta samun rahotannin faɗa a gabashi da arewacin birnin, wanda ya haifar da tagayyarar mutane 36,000," ta kuma ƙara da cewa "Adadin farar hula da suka hallaka zai iya haura haka sosai."

Ta kuma yi gargaɗin cewa, "Rikicin yana barazana ga farar-hula 800,000 da ke zaune a el-Fasher. Kuma zai iya janyo ƙarin faɗa a wasu sassan Darfur".

DiCarlo ta ƙara da cewa yaƙi a el-Fasher "zai iya haifar da ƙazamin faɗan ƙabilanci a gabaɗaya Darfur", kuma ya kawo cikas kan rarraba kayan agaji a yankin" da tuni yake fuskantar barazanar yunwa."

Tun shekaru 20 da suka gabata yankin Darfur ya yi fama da tsarin gallazawa daga Janjaweed — wata ƙungiyar mayaƙa da tuni ta shige cikin rundunar RSF.

Alƙaluma masu firgitarwa

A cewar ƙungiyar Doctors Without Borders [ko MSF], sama da mutane miliyan 8.4 sun bar gidajensu tun lokacin da yaƙi ya ɓarke a Sudan ranar 15 ga Afrilun bara, inda kusan mutane miliyan 1.8 suka ƙauracewa ƙasar.

Ƙiyasi ya nuna cewa kusan mutane 15,000 aka kashe zuwa yanzu a yaƙin, kuma MDD ta ruwaito kwanan nan cewa dubban mutane suna ta barin ƙasar a kullum.

Duk da yawan wannan adadi, martanin ƙasashen duniya ya yi rauni, sakamakon cewa kashi biyar cikin ɗari kacal na buƙatun kayan agaji aka iya tarawa, a cewar ƙungiyoyin agaji.

An gudanar da zagaye da dama na tattaunawar sulhu, yawanci bisa shiga-tsakani daga Saudiyya da Amurka, amma yunƙurin ya gaza kawo ƙarshen ɓarin wuta.

TRT Afrika da abokan hulda