Matakin da jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta dauka na ayyana Honarabul Abbas Tajuddeen daga Jihar Kaduna a matsayin wanda take so ya zama shugaban majalisar wakilan kasa da Ben Kalu daga Jihar Abia a matsayin mataimakinsa ya bar baya da kura.
A ranar Litinin ne jam’iyyar ta fitar da sunayen 'yan majalisar dokokin da take so su zama shugabannin majalisun dokokin kasar ta 10 bayan da, a cewarta, ta tuntubi zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A bangaren majalisar dattawa, APC ta zabi Sanata Godswill Akpabio da Barau a matsayin wadanda take su zama shugaba da mataimakinsa.
Sai dai matakin da ta dauka a majalisar wakilai bai yi wa wasu manyan 'yan majalisa dadi ba, abin da ake gani zai iya haddasa rikici.
Tuni wasu daga cikin wadanda suke zawarcin kujerar suka hau dokin na-ki inda suka yi watsi da matakin jam’iyyar.
Wadanda suke zawarcin kujerar shugaban majalisar tarayyar da suka ki amincewa da wannan mataki sun hada da Honarabul Idris Wase da Alhassan Ado Doguwa da Sada-Soli Jibiya. Sauran sun hada da Honorabul Mukhtar Betara da kuma Ahmed Jaji.
‘Hakkinmu ne zaben shugaban majalisa’
Wasu daga cikin zababbun ‘yan majalisar wakilan Nijeriya wadanda suka nuna rashin jin dadinsu dangane da matakin Jam’iyyar APC sun gudanar da wani taro a Abuja a ranar Litinin.
Sun kwatanta wannan mataki da uwar jam’iyyar ta dauka a matsayin yunkurin yi musu dauki-dora.
Cikin mahalarta taron har da Honarabul Wase da Ado Doguwa da Yusuf Gagdi and Sada-Soli da Mohammed Monguno.
Honorabul Wase shi ne mataimakin kakakin majalisar tarayya, kuma ya bayyana cewa wanda Jam’iyyar APC ta zaba, Abbas Tajuddeen, ba mutum ba ne da ‘yan majalisa suka sani sosai.
Ya caccaki matakin da APC ta dauka inda ya ce bai kamata a dauki irin wannan mataki ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.
Shi ma Alhassan Ado Doguwa, wanda a yanzu shi ne shugaban masu rinjaye, ya bayyana cewa dole ne a bar majalisar ta rika zabar shugabanninta.
Ya bayyana cewa hakkinsu ne zabar shugaba a majalisa kuma bai kamata wasu daga waje su rika zaba mata shugaba ba.
“Wani sako da nake son aikawa shi ne majalisa wuri ne da dole ne a bari ya rinka zaba wa kansa shugaba. Batun wanda zai jagorance mu, wata matsala ce wadda ta shafe mu, mu kadai ba matsalar wani bace,” in ji Doguwa.
Rikicin shugabancin majalisa a Nijeriya
A 2011, an ga yadda aka yi ta kai ruwa rana tsakanin ‘yan majalisar tarayya a Jam’iyyar PDP inda har Aminu Waziri Tambuwal ya zama kakakin majalisar tarayya.
A lokacin, Tambuwal ya fafata da Mulikat Akande-Adeola inda ya samu kuri’u 252 yayin da ita kuma ta samu kuri’u 90.
Sa’annan an ga yadda aka samu rabuwar kai a Jam’iyyar APC mai mulki a 2015 da kuma yadda ‘ya’yan Jam’iyyar APC a majalisar suka bijire wa zabinta suka zabi Honarabul Yakubu Dogara a maimakon Femi Gbajabiamila.
Yakubu Dogara ya samu kuri’u 182 sai kuma Gbajabiamila ya samu kuri’u 174.
Hakan ne ya sa masu sharhi a siyasa ke ganin ya kamata APC ta bar 'yan majalisar su zabi wadanda suke so su jagorance su kada wasu daga cikinsu su hada kai da 'yan jam'iyyun hamayya don ba ta kunya.