Wani sabon rahoto da aka fitar a jiya Laraba ya ce masu ikirarin jihadi da ke ayyukansu a yankin Sahel sun samu matsuguni a arewacin Nijeriya bayan da suka shiga ƙasar daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Benin.
Rahoton na cibiyar bincike ta Clingendael ya ce an yi amanna masu ikirarin jidadin da suke da alaƙa da ƙungiyar al-Qaida sun tsallaka arewacin Nieriya daga Benin inda suka samu mazauni a Gandun Daji na Tafkin Kainji, ɗaya daga cikin wurare mafi girma a ƙasar.
Yankin ya kasance wajen da wasu ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar bayan ke “cin karensu babu babbaka.“
"Hakan na zuwa ne a wani sabon lamari da masu ta da ƙayar bayan ke komawa ƙasashen Yammacin Afirka masu arziki da ke kusa da gaɓar teku,” kamar yadda cibiyar wadda ta yi zuzzurfan bincike kan lamarin ta bayyana.
Mazauna kusa da gandun dajin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa wajen, wanda yawan zakunan da ke cikinsa ke raguwa sosai-sosai, ya fi shekara ɗaya a rufe saboda barazanar rashin tsaro daga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ke kai hare-hare a ƙauyuka da kan tituna.
“A da wajen tamkar cibiyar yawon buɗe ido yake amma a yanzu, da wuya mutane su iya ko da wucewa ne,” in ji John Yerima, wanda ke zaune a garin Bussa kusa da gandun dajin.
“A yanzu ba za ka iya bi ko da ta kusa da titin da zai kai ka wajen ba. Yana da hatsari sosai,” in ji Yerima.
Daya daga cikin waɗanda suka wallafa rahoton kuma babban mai bincike na cibiyar Kars de Bruijne, ya ce yanayin tsaro a gandun dajin mai fadin murabba'in kilomita 5,300 a jihar Neja da kuma kan iyakar kasar da Benin "yana wuce iyaka" kuma "al'amari ne mai muni fiye da yadda muke zato."
Zaman ƙungiyoyin masu tada ƙayar baya a gandun dajin shi ne alama ta farko da ke nuna alaƙa tsakanin masu tsaurin ra’ayi ‘yan ƙasar da suka daɗe suna ayyukansu a arewaci da kuma mayaƙan al-Qaida daga Sahel, in ji, Bruijne.
Ya ƙara da cewa kasancewarsu a wajen yana ba da dama ga masu tsattsauran ra'ayi na samun gagarumar nasara a kasashen biyu, wadanda tuni suka fuskanci munanan hare-hare a 'yan shekarun nan.
Rahoton na Clingendael ya ce ba a san ko mene ne manufar masu tsattsauran ra'ayi na yankin Sahel da ke dajin da kuma yadda alakarsu da sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai za su kasance ba.
James Barnett, wani jami'in Cibiyar Hudson da ke aiki a arewa maso yammacin Nijeriya ya ce "Masu ikirarin Jihadi na Sahel na iya kokarin yin amfani da yankin arewa maso yammacin Nijeriya a matsayin wurin tattara kudade da dabaru da kuma kokarin yin tasiri ga kungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke can a matsayin wani bangare na gasarsu."
Kiyaye muhalli
Akwai kuma damuwa daga masu rajin kare muhalli da dabbobi cewa kasancewar kungiyoyin da ke dauke da makamai a dajin na iya kara yin barazana ga sauran zakuna da yawansu ya ragu sakamakon farauta da sauyin yanayi.
Sun ce babu jami’ai masu sintiri sosai a gandun daji da kuma kare dabbobin wajen, wanda hakan ya sa kungiyoyin masu dauke da makamai ke kai musu hari cikin sauki.
"Baya ga munanar yanayin tsaro a yankin, akwai kuma damuwa game da batun raguwar zakuna a gandun dajin," in ji Stella Egbe, babbar manajar a gidauniyar kiyaye gandun daji ta Nijeriya.