Majalisar Dattijan Nijeriya ta jingine batun ƙudurin dokokin haraji na Nijeriya da ake taƙaddama a kansu.
Mataimakain Shugaban majalisar Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da haka, yayin da yake jagorantar zamar majalisar ta dattawa a ranar Laraba.
Sanata Barau ya ce an jingine batun ne saboda yadda ake ce-ce-ku-ce a kan ƙudurorin, da kuma tabbatar da cewa an yi duban tsananki kan ɓangarorin da wasu al’ummar ƙasar ke nuna damuwa a kai.
Ya ƙara da cewa an kafa wani kwamiti na majalisar dattijai ƙarƙashin Sanata Abba Moro da zai zauna da ofishin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’ar Ƙasar don duba ɓangarorin da suke janyo taƙaddama don a warware su.
“Mun yanke hukuncin jingine batun siyasa da ɓangaranci da ƙabilanci a gefe, mu zauna mu-ya-mu, don mu lalubo mafita kan batun Ƙudurorin Gyara kan Dokokin Haraji,” a cewar Sanata Barau.
“Mun sanar da ɓangaren zartarwa matsayarmu, kuma an amince cewa za a kafa wani kwamiti da zai zauna ya yi duba kan ɓangororin da ake taƙaddama a kansu don a warware su.”
Mataimakin shugaban na majalisar dattijai ya ce kwamitin, na da wakilai daga dukkan shiyyoyin ƙasar guda shida, da wasu kwamitoci da suka shafi kuɗi da banki da kasafin kuɗi na majalisar, da ma duka shugabannin majalisar, inda za su fara tattaunawa da Ministan Shari’a a ranar Alhamis.
Ya ce an ɗauki matakin ne "domin ƙasar ta Nijeriya ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya."
“Za mu warware dukkan batutuwan kafin a bar komai ya wuce,” in ji Sanata Barau.
Sai dai Majalisar ta Dattijai ba ta bayyana lokacin da ɓangaranta da na ofishin Ministan Shari’ar ƙasar za su kammala tattaunawa kan batun ba.
Tun lokacin da shugaban Nijeriya ya aike da ƙudurori huɗu don yin gyare-gyare kan dokokin harajin ƙasar, ake ce-ce-ku-ce kan wasu ɓangarorin dokokin, bisa zargin cewa sauye-sauyen za su shafi yadda wasu jihohin ƙasar ke samun kuɗi daga rabon arzikin ƙasar da ake yi a duk wata.
Ɓangaren da ya fi jan hankali shi ne yadda za a sauya tsarin rabon harajin VAT, abin da wasu ke zargin cewa za a fifita wasu tsirarun jihohi a ƙara azurta su, yayin da za a ƙara talauta mafi yawan jihohin ƙasar.