Kotun Ƙolin Nijeriya ta ce naɗin da gwamnoni suke yi wa shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, yana mai cewa alhakinsu ne su gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

Kotun Ƙolin Nijeriya ta umarci gwamnatin tarayya ta riƙa bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai-tsaye ba tare da sun shiga hannun gwamnatocin jihohi ba.

Alƙalin Kotun Mai Shari'a Emmanuel Agim ya bayar da umarnin ne a hukuncin da ya yanke ranar Alhamis a Abuja, babban birnin ƙasar.

Kotun ta ce matakin da gwamnatocin jihohi suka ɗauka na riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi a hannunsu ya saɓa wa kudin tsarin mulkin Nijeriya.

Mai Shari'a Agim ya umarci gwamnatin tarayya ta riƙa tura wa ƙananan hukumomin ƙasar 774 kuɗaɗensu kai-tsaye domin su riƙa gudanar da harkokinsu.

Kazalika alƙalin ya ce naɗin da gwamnoni suke yi wa shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, yana mai cewa alhakinsu ne su gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya tana samun kashi 52.68, yayin da gwamnatocin jihohi suke samun kashi 26.72 na kuɗin da ake rabawa duk wata daga asusun rabon arzikin ƙasa.

Su kuwa ƙananan hukumomi, suna karɓar kashi 20.60 na kuɗin, sai dai gwamnatocin jihohi ne suke juya galibin kuɗaɗen, inda suke ajiye su a asusun haɗin-gwiwa tsakaninsu da ƙananan hukumomi.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ce ta shigar da ƙara inda ta roƙi Kotun Ƙolin ta bari a riƙa tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu ba tare da katsalandan ɗin gwamnoni ba.

TRT Afrika