Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja babban birnin Nijeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele.
Mai Shari’a Olukayode Adeniyi ya bayar da belin Emefiele ne a wani hukunci da ya yanke a yau Laraba inda ya ba da umarnin miƙa shi ga lauyoyinsa.
Sai dai alkalin ya umarci a sake gabatar da Emefiele a gaban kotun ranar 15 ga watan Nuwamban da muke ciki, inda alkalin farko da ya fara sauraron ƙarar da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzkin Nijeriya zagon kasa, EFCC ta shigar, zai ci gaba da shari’ar.
Alkalin ya kuma ce dole tsohon gwamnan Babban Bankin ya ajiye fasfonsa a kotun har zuwa lokacin da za a gama shari'ar.
Sannan kuma alkalin ya yi magana a kan cewa dole a kawo ƙarshen tsare mutane ba tare da yi musu shari'a ba.
Ya kuma ce bai kamata kotu ta ƙi yin duba a kan batun tsare shi da aka yi tsawon kwana 151 ba, sannan dole gwamnatin tarayya da Atoni Janar na ƙasar su bi umarnin kotu.
Waiwaye
A ranar 9 ga watan Yuni ne Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da shugaban Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN, nan take.
Kwana guda bayan nan ne hukumar tsaro ta DSS ta sanar da cewa Godwin Emefiele yana hannunta.
Sai kuma ranar 13 ga watan Yuli DSS ɗin ta ce ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa sabbin zarge-zargen aikata laifuka.
Wani labari mai alaƙa
Zamanin Emefiele
An nada Emefiele a matsayin shugaban Babban Bankin Nijeriya ne a 2014 bayan an dakatar da Sanusi Lamido Sanusi.
Godwin Emefiele ya aiwatar da sauye-sauyen da suka jawo ce-ce-ku-ce a fannin tattalin arzikin Nijeriya.
A watan Oktoban 2022, ya sauya fasalin takardun naira 200, 500 da kuma 1,000 da zummar rage hauhawar farashin kayayyaki da yin kudin-jabu da kuma biyan kudi ga masu garkuwa da mutane.
Sai dai matakin ya jefa 'yan kasar cikin mawuyancin hali sannan 'yan siyasa sun bayyana cewa an fito da shi ne da zummar cin zarafinsu.