An samu ƙaruwar rashin tsaro a Nijeriya da kashi 12.02 cikin 100 a watan Janairu idan aka kwatanta da na Disamban bara, a cewar sabon rahoton Kamfanin Tattara Bayanai kan Tsaro na Beacon a ƙasar, duk da ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke yi na daƙile miyagun ayyuka.
Sabon rahoton da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa munanan al’amuran rashin tsaro 727 ne suka faru a watan Janairu, inda aka kashe mutum 1,022, lamarin da ke nuna ƙaruwa da kashi 15.88 cikin 100 idan aka kwatanta da Disamban bara.
“Ita ma satar mutane ta yi matuƙar ƙaruwa da kashi 39.88 cikin 100 idan aka kwatanta da na rahoton Disamban 2023. An yi garkuwa da jumullar mutum 726 a faɗin ƙananan hukumomi 250 a jihohin ƙasar 36 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja,” a cewar Kamfanin Tsaro na Beacon.
Rahoton ya koka kan yadda aka samu ƙaruwar abubuwa marasa daɗi a duk ma’aunan tsaro na watan Janairu idan aka kwatanta da bara war haka, “duk kuwa da gagarumin ci gaba da aka samu a cikin ƙoƙari da ayyukan da jami’an tsaro ke yi wajen yaƙi da rashin tsaro a Nijeriya."
Sabbin bayanan sun fayyace cewa ɓangaren al’umma da abin ya fi shafa su ne fararen hula, inda wasu ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da suka haɗa da ƴan fashi da makami a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya suke zama manyan masu aikata laifin.
Rahoton ya kuma faɗi irin dabaru da hanyoyin da waɗannan ƙungiyoyi suka ɗauka, ta yadda hukumomin tsaro za su sake fahimtar yadda za a shawo kan lamarin.
“Jihar Zamfara ce kan gaba a yawan mutanen da aka yi garkuwa da su a Janairu, inda aka sace mutum 177, sai Kaduna mai 133, yayin da Babban Birnin Tarayya, Abuja yake biye da yawan mutum 73,” a cewar rahoton.
Ya fayyace cewa a Babban Birnin Tarayyar ma masu aikata miyagun laifuka da ƴan bindiga ne suke aikata waɗannan sace-sace na garkuwa da mutane.
Bugu da ƙari, a yankin Kudancin ƙasar kuma, fuskantar yanayi masu hatsari ya taimaka matuƙa wajen jawo yawan asarar rayuka da jikkata fararen hula.
Da yake yin tsokaci a kan rahoton, Shugaban Kamfanin Tsaro na Beacon Dokta Kabiru Adamu, ya ja hankali kan yadda ake amfani da bayanai wajen bin diddigin abubuwan tsaro a matsayin wani makami na sarrafa tsaro da saka hannun jari wajen inganta tsarin leƙen asiri.
Dokta Adamu ya yi kira ga ɓangaren Zartarwa da Majalisu da su yi amfani da tsarin da ya dace ta hanyar amfani da ma'auni, tare da goyon bayan ingantaccen tsarin sa ido da ƙimantawa, wanda zai tabbatar da ƙarfinsu wajen aiwatar da kasafin kudi a dukkan ɓangarori, da kuma ƙoƙarin kawar da wannan matsala ta hanyar gano tushenta.