A sansanin masu sana'ar da yake a birnin Yamai a Jamhuriyyar Nijar, ana yin takalma da sauran ababuwan kwalliya /Hoto: TRT Afrika Hausa
Mutanen da ke aiki a sansanin sun dukufa wajen sarrafa abubuwa masu amfani ga mutane /Hoto:TRT Afrika Hausa
Abubuwan da ake sarrafawa da fata suna da yawa ba jakankuna ba ne kawai /Hoto: TRT Afrika Hausa
Ana amfani da fatar rakumi da ta shanu da ma ta kananan dabbobi wajen sarrafa kayayyaki na kawa /Hoto:TRT Afrika
Ciniki a sansanin ya samu koma baya a lokacin annobar korona inda masu yawon bude ido da suka fi sayen kayayyakin suka daina zuwa /Hoto:TRT Afrika Hausa
Matsalar tsaro ma ta taka rawa wajen rage yawan masu yawon bude ido da ke shiga kasar, lamarin da ke rage yawan cinikin da ake yi a sansanin /Hoto:TRT Afrika Hausa
Dukawan da ke aiki a sansanin sun haura 200 /Hoto:TRT Afrika Hausa
Kayayyaki iri-iri ake samarwa a sansanin/ Hoto:TRT Afrika Hausa
Kashi 90 cikin 100 na ayyukan da hannu ake yi /Hoto: TRT Afrika Hausa
Sansanin ya kasance wani wuri inda dukawan ke bayyana irin tasu basiran ga duniya /Hoto: TRT Afrika Hausa
TRT Afrika