Jirgin ruwa na dakon kaya mafi girma a Yammacin Afirka wato MV "Great Lagos" ya sauka a tashar jiragen ruwa ta PTML da ke Lagos, a kudu maso yammacin Nijeriya a ranar 1 ga Disamban 2023.
An yi bikin murnar zuwan jirgin a ranar Litinin, lamarin da ya tara masu ruwa da tsaki a masana'antar sufurin jiragen ruwa, da fiton kayayyaki daga ciki da wajen Nijeriya.
A yayin taron, masu ruwa da tsakin sun ce samuwar jirgin ruwa na Roro a nahiyar wanda a baya ba a taɓa ganin irinsa ba, zai saukaka harkokin kasuwanci da inganta harkokin kasuwanci da ma haɓɓaka tattalin arziki a Nijeriya da Afirka baki daya.
Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da jirgin a Legas, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-olu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Obafemi Hamzat, ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na samar da ingantaccen yanayin kasuwanci ga masu zuba jari na gida da waje.
"Abin farin ciki ne a gare ni na shiga cikin gudanarwar rukunin kamfanin Grimaldi, waɗanda fitattun masu ruwa da tsaki ne a harkar sufurin jiragen ruwa a wannan da ma gagarumin shirin isowar jirgin mai suna "MV Great Lagos".
"Ba sunan jihar mu da aka bai wa jirgin kaɗai ne ya fi burge mu ba, wannan babban jirgin ruwa alama ce da ke nuni da ƙarfi da kuzarin da ake samu a nahiyar tekunmu, haƙiƙa wannan lamari ne mai matukar muhimmanci.
"Yau ranar farin ciki da alfahari ce a gare mu domin wannan biki ya nuna wani sabon babi a tarihin teku a nahiyarmu, ba jihar Legas kadai ba, har ma da faɗin kasarmu baki ɗaya".
Ya ce jirgin ruwan, mallakar rukunin kamfani na Grimaldi, alama ce ta ƙwarewar kamfanin a ɓangaren hada-hada a teku; da kuma zurfin dangantaka mai ɗorewa tsakanin rukunin kamfanin da jihar Legas.
"A kan haka, ina mika godiyata ga rukunin kamfanin Grimaldi bisa jajircewar da suka yi a jiharmu, wannan yunƙuri ya shaida yadda kuka amince da tattalin arzikinmu da kuma karfin al'ummarmu.
"Mun gode da yadda kuka sanya hannun jari, musamman ta hanyar al'amuran da suka shafi sufurin jiragen ruwa a teku a tashar jiragen ruwa ta PTML, gudunmawarku tana ƙarfafa matsayinmu a matsayin cibiyar tattalin arziƙi mai muhimmanci kuma wata hanyar shiga nahiyar Afirka baki ɗaya," in ji Gwamna San-olu.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Legas ta himmatu domin samo dabarun mayar da Legas jiha mai karfin tattalin arziki na karni na 21, ta hanyar samar da yanayi mai dacewa tare da samar da kayayyakin more rayuwa don ƙara ƙarfin tattalin arziki a nahiyar tekun.
"Ƙarfin tashar jiragen ruwa mai zurfi da ke Badagry da ake ginawa a yanzu, tare da tashar ruwa mai zurfi da ke Lekki da tuni aka fara aikinsu, za su inganta matsayin jihar Legas a matsayin cibiyar kasuwancin teku a ƙasashen Afirka," in ji Gwamnan na Legas.
Jirgin ruwan na MV 'Great Lagos' yana da ƙarfin ɗauka tare da jigilar motoci 2,500 da kwantena 2,000 ɗauke da kayayyaki.