Kotun Soji ta Nijeriya ta sanya ranar Talata 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a yanke wa wani babban jami’inta Manjo Janar Umaru M Mohamed hukunci bayan samun sa da laifukan almundahana.
Wata ta tawaga ta musamman ta alkalai bakwai karkashin jagorancin Manjo Janar James Myam ce ta jagoranci shari’ar, inda ta samu Manjo Janar Mohammed, wanda shi ne shugaban Kamfanin Kadarorin Rundunar Sojin Nijeriya, da laifi 14 daga cikin 18 da ake tuhumar sa da su.
Laifukan sun haɗa da sama da fadi da kudade da kitsa tuggu da yin jabun takardu da karkatar da wasu kadarorin rundunar sojoji da kuma wasu sauran laifukan.
A lokacin da yake karanta ƙarar, Janar Myam ya bayyana cewa “A kan tuhuma ta farko zuwa ta shida da suka haɗa da almundahana da kuɗi daga masu jiragen ruwa a Marina da ke Lagos, an samu Manjo Janar UM Mohammed da laifi.
“Sannan an same shi da laifi a kan tuhuma ta takwas da ta ƙunshi yin jabun takardu da sunan daraktocin Kamfanin Kadarori na Rundunar Sojin.
Sai kuma aka same shi da laifi kan tuhuma ta tara ta laifin ƙin ɗaukar mataki kan cin amanar ƙasa,” in ji Janar Myam kamar yadda Gidan Rediyon Voice of Nigeria ya rawaito.
Kazalika tawagar masu shari’ar ta ce an ƙara samun janar ɗin da laifi a kan tuhuma ta 10 ta yin jabun takardu.
Sayar da ƙadarori
A tuhuma ta 12 kan batun sayar da ƙadarorin kamfanin da yake jagorantar kuwa, tawagar shari’ar ta samu Janar Mohammed da laifin sayar da ƙadarorin kamfanin a kan naira miliyan 200, bayan da ya daina shugabantarsa.
Sai kuma tuhuma ta 13 da ak same shi da laifin ɗauke naira miliyan 74 daga asusun kamfanin ranar 22 ga watan Agustan 2019.
A hannu guda kuma, tawagar ta wanke Janar mohammed daga tuhuma ta 11 da ta 17, da ake zargin Janar din da cire naira miliyan 750 daga asusun kamfanin, inda tawagar ta ce masu shigar da ƙarar sun gaza bayar da gamsassun hujjoji kan zargin.
Tawagar ta alkalai bakwai dukkansu masu muƙamin Manjo Janar za ta yanke wa Manjo Mohammed hukunci ranar Talata mai zuwa, 10 ga watan Oktoban 2023.