Gwamnatin Nijeriya ta ware ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar dimokuradiyya domin tunawa da zaben da MKO Abiola ya yi ikirarin samun nasara wanda aka soke a 1993. Hoto/Bola Tinubu Facebook

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shi ma yana jin radadin da ‘yan kasar ke ji bayan cire tallafin man fetur.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a jawabin da ya yi na zagayowar ranar Dimokuradiyya ta 12 ga watan Yuni.

A zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne aka ayyana 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokuradiyya domin tunawa da zaben 1992 wanda Cif MKO Abiola ya yi ikirarin samun nasara amma aka soke shi.

A yayin jawabin, Shugaba Tinubu ya ce an dauki matakin cire tallafin ne domin ceto Nijeriya.

“Na yarda cewa wannan matakin zai kara dora nauyi kan jama’ar kasarmu. Ina jin radadin da kuke ji. Wannan na daga cikin matakan da suka kamata mu yi hakuri da su domin ceto kasarmu daga faduwa da kuma karkatar da arzikinmu daga wasu tsirarun mutane marasa kishin kasa,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban kasar ya kuma roki jama’ar Nijeriya su kara hakuri da sadaukarwa kadan domin kasar ta ci gaba da tafiya daidai.

Tun da farko, Shugaba Tinubu ya soma ne da magana kan zaben 12 ga watan Yuni wanda Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola ya yi ikirarin samun nasara inda ya ce gwagwarmayar da ‘yan kasar suka soma tun a lokacin ita ce ta haifi dimokuradiyyar da ake cin gajiyarta a halin yanzu.

“Rashin adalcin da aka yi na soke zaben da aka tabbatar na gaskiya da adalci ne ya zama wani kalubale da ya sa kungiyoyi masu zaman kansu suka jajirce wurin samun ‘yancin kanmu a karo na biyu ta hanyar komawar gwamnati mulkin dimokradiyya a 1999,” in ji Tinubu.

Shugaba Tinubu ya yi jinjina matuka ga marigayi Abiola inda ya ce ya bayar da ransa ga Nijeriya domin dimokradiyya ta tabbata.

Shugaba Tinubu ya ce ba za a yi tuya a manta da albasa ba domin kuwa akwai wasu muhimman mutane wadanda su ma ba za a manta da su ba da suka bayar da rayuwarsu domin dimokuradiyya a Nijeriya.

“A kullum a irin wannan rana tsawon shekaru, za mu ci gaba da tunawa da jaruman dimokuradiyya kamar Kudirat Abiola, matar Cif Abiola, wadda aka yi mata kisan gilla a lokacin da take yi wa jama’a gwagwarmaya.

“Za mu tuna da Pa Alfred Rewane, daya daga cikin jaruman da suka yi gwagwarmayar dimokradiyya da Manjo Janar Shehu Musa Yar’Adua (mai ritaya) wadanda sojojin rikon kwarya suka kawar a yayin gwagwarmayar dimokradiyya,” a cewar Shugaba Tinubu.

Shugaba Tinubu ya kara jaddada cewa kada a kuskura a yi wasa da dimokuradiyya inda ya ce akwai bukatar a kowane lokaci a rinka tattalinta kamar kwai.

Ya kuma ce jama’a ba za su taba sanin darajar abu ba sai sun rasa shi.

TRT Afrika