Hukumomin tsaron Nijeriya sun bayyana cewa suna neman tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Adoza Bello ruwa-a-jallo sakamakon yunƙurin kauce wa tuhuma kan zargin almundahanar sama da Naira biliyan 80.
A tsakiyar makon nan ne Hukumar Yaƙi da Masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa (EFCC) ta shirya gurfanar da tsohon gwamnan na Jihar Kogi a gaban kotu, amma ya ƙi gabatar da kansa.
'Muna neman Bello ruwa-a-jallo'
Tun da fari dai Hukumar EFCC ce a ranar Alhamis ta fitar da sanarwar neman tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ruwa-a-jallo.
EFCC ta ce ana zargin gwamnan da almundahanar kuɗaɗen al'umma da suka kai Naira biliyan 80.2 a lokacin yana jagorancin jihar.
Sanarwar da EFCC ta fitar mai ɗauke da cikakken suna da hoton Yahaya Adoza Bello ta ce "Ana sanar da dukkan jama'a cewa Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Nijeriya zagon ƙasa (EFCC) tana neman Yahaya Adoza Bello, tsohon gwamnan Jihar Kogi da hotonsa yake nan sama ruwa-a-jallo bisa zarginsa da almundahanar kuɗi da ya kai naira biliyan 80.2."
Sanarwar da Shugaban Sashen Hulda da Jama'a na EFCC Dele Oyewale ya sanya wa hannu ta ƙara da cewa "Bello, mai shekara 48, ɗan ƙabilar Ebira ne da ya fito daga ƙaramar hukumar Okene ta jihar Kogi, kuma wajen da aka gan shi a karo na ƙarshe shi ne gida mai Lamba 9, Benghazi Street, Wuse Zone 4, Abuja."
Ban yarda da zargin da ake yi min ba
A ranar Alhamis ɗin nan Hukumar EFCC ta garzaya gaban kotu inda ta shigar da ƙarar tsohon Gwamna Bello.
Amma lauyan tsohon gwamnan Abdulwahab Mohammed ya ƙalubalanci gurfanar da wanda yake wakilta a gaban Babbar Kotun Tarayya kan batun hurumi, yana mai cewar bai aikata laifin komai ba.
Wannan lamari na zuwa ne bayan da EFCC ta samu umarni daga Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, wadda ta buƙaci a kama tsohon gwamnan wanda ya tsere.
Gwamnan kogi Adodo ya ɗauke ubangidansa
A ranar Laraba ne jami'an Hukumar EFCC suka tare hanyoyin zuwa gidan tsohon gwamnan na Kogi Yahaya Bello, inda daga bisani suka yi yunƙurin kama shi.
Amma a wani yunƙuri da ba a saba gani ba, gwamnan Jihar Kogi Mai ci Ahmed Usman Ododo ya je da tawagarsa gidan Bello inda ya ɗauke ubangidansa zuwa Lokoja, babban birnin jihar.
Kafafen yaɗa labarai na Nijeriya sun ruwaito cewa an ji ƙarar harbe-harbe a kusa da gidan a lokacin da lamarin ke faruwa.
Bayan afkuwar lamarin, Hukumar EFCC ta sanar da cewar hana jami'anta gudanar da aikinsu babban laifi ne da ka iya kaiwa ga ɗaure mutum.
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta janye jami'anta da ke tsaron Bello
A ranar Alhamis, rundunar ƴan sandan Nijeriya ta sanar da cewar ta janye jami'anta da ke tsaron lafiya tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.
Wani saƙo da rundunar ƴan sandan ta fitar ta hannun Mataimakin Sufeto Janar na Ƴan sandan Nijeriya da ke kula da 'Yan sandan Kwantar da Tarzoma a Abuja zuwa ga Cibiyar jami'an Kwantar da Tarzoma ta (Mopol 37, Lokoja) ta buƙaci a janye jami'an ƴan sandan da ke tsaron lafiyar Bello nan-take.
A saƙon, an bayyana cewa "Rundunar Ƴan sandan ta bayar da umarnin janye dukkan jami'an tsaron da ke tare da Mai Girma Alhaji Yahaya Bello, tsohon gwamnan Jihar Kogi."
Saƙon ya bayar da umarni da lallai a zartar da wannan umarni ba tare da ɓata lokaci ba.
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya na neman tsohon gwamna Bello
A nata ɓangaren, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya ta bayyana cewa daga yanzu tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello na jerin sunayen waɗanda take nema ruwa-a-jallo.
Sanarwar da Hukumarr ta fitar mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Kwanturola DS Umar ta sanar da dukkan cibiyoyinsu na shiyyoyi da kan iyakoki cewar daga yanzu suna neman tsohon gwamnan Kogi Bello.
Sanarwar ta bukaci jami'an Hukumar Shige da Ficen da su kama Yahaya Bello matukar suka gan shi a kan iyakokin Nijeriya, sannan a mika shi ga Daraktan bincike na hukumar ko a kira lambobin waya kamar haka 08036226329 /07039617304.
Ministan Shari'a ya buƙaci Bello ya miƙa kansa
Ministan Shari'a kuma Babban Atoni na Nijeriya Lateef Fagbemi (SAN) ya yi kira ga tsohon gwamnan na Jihar Kogi da ya miƙa kansa ga hukumomi.
A wata sanarwa da Ministan ya fitar a ranar Alhamis, ya soki matakin Yahaya Bello na ƙin gabatar da kansa ga hukuma.
Sanarwar ta ce "Dambarwar da ta auku a lokacin da Hukumar EFCC ke ƙoƙarin sauke nauyin da doka ta ɗora mata ta ja hankalina cike da sanya damuwa. A bayyana yake ƙarara a yanzu an bai wa Hukumar EFCC cikakkiyar damar gayyatar kowanne mutum a yayin da take gudanar da bincikenta ko ayyukanta."
Ministan ya jaddada cewar guje wa doka ba zai warware wata matsala ba, sai dai ma ya ta'azzarata.
"Ya zama dole a bai wa irin waɗannan hukumomi hurumin gudanar da ayyukansu... Kuma ina kira ga dukkan wani da Hukumar EFCC ko wata hukuma ta Nijeriya ta gayyata da ya miƙa kansa. Maimakon wasan-ɓuya da ƙoƙarin guduwa wanda hakan na iya rage ƙimarmu a idon duniya," in ji Minista Fagbemi.