Kwamitin gwamnatin tarayya da ke rabon arziƙin ƙasa wato FAAC, ya ce ya raba naira tiriliyan 1.2 ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomin Nijeriya waɗanda kuɗi ne da aka samu a matsayin kuɗaɗen shiga a watan Agusta.
Kwamitin ne ya sanar da hakan bayan kammala taron da ya gudanar na watan Satumba a Abuja.
Sanarwar da mai magana da yawun ofishin akanta janar na Nijeriya Bawa Mokwa ya fitar a ranar Talata, ta ce kuɗin da aka raba a wannan karon sun ragu da kashi 11 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda aka raba a watan Yuli.
A watan Yulin bana an raba naira tiriliyan 1.358 wanda hakan ke nufin an samu raguwa da naira biliyan 155.
Ofishin akanta janar ɗin ya bayyana cewa kuɗaɗen shigar sun haɗa da waɗanda aka samu daga kamfanoni wanda ya kai naira biliyan 186.636 da na haraji kan kayayyaki wanda ya kai naira biliyan 533.895 da wanda aka samu daga ɓangaren tura kuɗi ta banki wanda ya kai naira biliyan 15.02 da haraji kan bambancin kuɗi da ya kai naira biliyan 468.25.
Bawa ya kara da cewa daga cikin naira tiriliyan 1.203 da aka raba a matsayin kuɗin shiga, gwamnatin tarayya ta samu jimillar kudi naira biliyan 374.93 sannan gwamnatocin jahohin sun samu jimillar kudi naira biliyan 422.86.
Sai kuma kananan hukumomi sun samu jimillar kudi naira biliyan 306.53 kuma an raba jimillar naira biliyan 99.47 (kashi 13 na kudaden shiga na ma’adinai) da jihohin da suka amfana a matsayin kudaden shiga.