Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne a shirye-shiryen shigowar watan Ramadana. / Hoto: Abba El Mustapha

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayar da umarnin rufe duk wani gidan gala da ake da shi a jihar.

Shugaban hukumar Abba El Mustapha ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

“A shirye-shiryen ta na shigowar watan Azumin Ramadana, Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta jihar Kano ta bayar da umarnin kulle dukkannin gidajen Galar da ke fadin jihar Kano,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Hukumar ta ce ba ta ɗauki wannan mataki ba sai da ta zauna ta tattauna da jagororin musu gidajen galar da ke jihar.

Hukumar ta ce dokar za ta fara aiki ne tun daga yau Lahadi har zuwa 1 ga watan Shawwal wato ranar bikin Ƙaramar Sallah.

A sanarwar, Abba El-mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji karya doka inda ya ce duk wanda hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar to hakika za ta dauki mataki mai tsauri a kansa wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na din-din-din.

TRT Afrika