Sojojin Nijeriya sun jima suna yaƙi da masu fafutikar kafa ƙasar Biafra ta IPOB a kudancin Nijeriya. / Hoto: Reuters

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta bayar da ladar miliyan 25 ga waɗanda suke da bayani dangane da waɗanda suka kashe sojoji biyar a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan wasu ‘yan bindiga a ranar Alhamis sun kai hari wani shingen bincike na sojoji da ke Obikabia a Ƙaramar Hukumar Obingwa ta Jihar Abia inda suka ƙona wurin tare da wata motar sintiri ta sojojin.

An bayyana cewa wasu daga cikin sojojin sun tsira daga harin da ‘yan bindigan suka kai.

Baya ga sojojin biyar da aka kashe, akwai ƙarin farar hula shida da suka rasu yayin harin, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta tabbatar.

“Gwamnatin jiha za ta bayar da ladar miliyan 25 ga duk wani wanda ya bayar da bayanai dangane da ɗaya daga cikin masu hannu a wannan kisan, kamar yadda sanarwar da kwamishinan watsa labarai da al’adu na Jihar Abia Okey Kanu ta bayyana.

A nata ɓangaren, ita ma Rundunar Sojin Nijeriya ta yi Allah wadai da wannan harin inda ta lashi takobin ɗaukar mummunan mataki kan masu hannu a wannan kisan.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma rundunar ta zargi haramtacciyar kungiyar 'yan awaren Biafra (IPOB) da ke son yankin kudu maso gabashin Nijeriyaya ɓalle daga ƙasar.

TRT Afrika