Gwamnan Jihar Kano da ke Nijeriya Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitocin biyu da za su yi bincike kan ta'annati da dukiyar al'umma, da mutanen da suka bata da rikicin siyasa da suka afku a tsakanin 2015 da 2023.
A yayin da yake kaddamar da kwamitocin a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Ana sa ran za su mika rahotonsu cikin wata uku.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ambato Gwamna Yusuf yana tunatar da cewa bincike kan ta'annati da dukiyar al'umma wani bangare ne na alkawarin da ya yi a lokacin da ake rantsar da shi.
Ya kara da cewa za a binciko tare a hukunta masu hannu a rikicin siyasa a jihar Kano musamman a zabukan 2023.
Sanarwar ta ruwaito gwamnan na cewa "Rikicin siyasa babban kalubale ne ga dimokuradiyya a duniya baki daya. Yana janyo asarar rayuka da dukiya, da ma janyo al'umma su ki amincewa da wadanda ke jagorantar su."
"Munanan kashe-kashen da aka yi na siyasa musamman a 2023 ba za su tafi haka kawai ba, za a dauki matakin ne don hana afkuwar hakan a nan gaba," a cewar gwamnan.
Kwamitin farko wanda yake karkashin Mai Shari'a Zuwaira Yusuf zai mayar da hankali kan rikicin siyasa da mutanen da suka bata tun daga 2015 zuwa 2023.
Gwamna Abba ya ce "Muna sa ran za su binciki munanan ayyukan, sannan su zakulo wadanda suke daukar nauyin rikicin. Su nemo tushen rikicin, sannan su gano yadda aka kitsa rikici a 2015, 2019 da 2023."
Da yake kaddamar da kwamiti na biyu karkashin Mai Shari'a Faruk Lawan, Gwamna Abba ya dora wa kwamitin alhakin gudanar da bincike kan ta'annati da dukiya da kadarorin al'umma.
Munanan kashe-kashen da aka yi na siyasa musamman a 2023 ba za su tafi haka kawai ba, za a dauki matakin ne don hana afkuwar hakan a nan gaba
Ya bukaci Ma Shari'a Lawan da dukkan mambobinsa kan kada su yi shayin bayyana duk wani waje da aka yi almundahana da dukiya ko kadarar al'ummar a lokacin mulkin gwamnatin da ta gabata a ciki da wajen jihar Kano.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa wannan mataki ba shi da alaka da siyasa ko nufar wasu mutane, aiki ne da ya dace da buktun jama'ar jihar Kano.
A yayin da yake kira ga kwamitocin da kar su kuskura su hada baki da wani, Gwamnan na Kano Yusuf ya kuma bukace su da su rike amana da aiki da rantsuwar da suka yi ta gudanar da aiki da gaskiya don yin adalci a jihar.
Gwamnan ya ce sai da aka yi tantancewa sosai kafin a zabi mambobin kwamitocin, kuma ya yi amanna za su yi aikin kamar yadda ake zato.
Ya ce "Mun yi duba ga tarihin ayyukanku, kuma ba mu samu wani daga cikin ku da rashin kirki ba. Mun amince da ku kuma muna fatan za ku mika rahotanninku a cikin watanni uku."