Jama'ar Maiduguri na barin gidajensu saboda ambaliyar ruwa a ranar 15 da Satumban 2024. / Photo: Reuters

Fiye da mutane 1,000 sun mutu yayin da aƙalla 740,000 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a Yammaci da Tsakiyar Afirka, inda ibtila'in ya shafi mutane sama da miliyan biyar a ƙasashe 16, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Alhamis ɗin nan.

Ɓangarori da dama na ƙasashen Tsakiya da Yammacin Afirka tare da yankin Sahel na fuskantar ambaliyar ruwa sosai saboda mamakon ruwan sama.

Ambaliyar ruwan ta fi yi wa Nijar da Nijeriya ɓarna inda suke da fiye da kashi 80 na waɗanda ibtila'in ya shafa, in ji Ofishin Ayyukan Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA).

Bugu da ƙari, dubban gidaje, makarantu da cibiyoyin kula da lafiya ma sun samu matsala, eka rabin miliyan na albarkatun gona ta lalace, abin da ka iya haddasa ƙarancin abinci musamman a Chadi da Nijar.

Wannan mummunan yanayi na barazanar haddasa ɓarkewar cututtuka, irin su kwalara da ka iya ɓulla a Nijeriya da Nijar, kamar MDD ta yi gargaɗi.

Joyce Msuya, mataimakin sakatare janar mai kula da ayyukan jinƙai ya ce, ofishinsu ya ware dala miliyan 35 don bayar da tallafi a Chadi, Nijar, Nijeriya, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Kongo Kinshasa. Sai dai kuma ana buƙatar ƙarin kuɗaɗe cikin gaggawa, in ji MDD.

A Nijeriya kawai, MDD ta ware dala miliyan biyar don taimaka wa mutane 280,000 da abinci, tsaftataccen ruwan sha da matsugunai, tare da ƙoƙarin kare ɓarkewar cutar kwalara.

Jami'ai sun ce kashi 46 kawai aka samu daga dala miliyan 927 na agajin gaggawa da ake buƙata a Nijeriya.

AA