Usman Baba Pategi  ɗa ne ga marigayi Etsu Usman Patako na Pategi./Hoto:OTHER

Fitaccen dan wasan kwaikwayo na Hausa Alhaji Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja ya rasu yana da shekara 81.

Bayanai daga iyalansa sun ce ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a birnin Kaduna da ke arewacin Nijeriya.

Alhaji Usman Baba Pategi ya taka rawa a matsayin Samanja Mazan Fama a wasan kwaikwaiyon da aka kwashe shekara da shekaru ana gabatarwa a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna.

An haife shi ranar 20 ga watan Mayu na shekara 1942 a Masarautar Pategi da ke Jihar Kwara.

Ɗa ne ga marigayi Etsu Usman Patako na Pategi.

Usman Baba Pategi ya yi karatun Firamare da Sakandare a Pategi da Ilorin.

A shekarun 1960 ya shiga Rundunar Sojin Nijeriya inda ya rike mukamin Kyaftin a lokacin yakin basasar kasar.

Ya yi ritaya a shekarar 1985 inda ya soma wasan kwaikwayo a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna, lamarin da ya ba shi damar rubutawa da kuma bayar da umarni na wasannin kwaikwayo. An fi saninsa a matsayin Samanja Maza Fama.

Baba Pategi yana da mata biyu da 'ya'ya.

TRT Afrika