Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu abin da ya samu Tinubu bayan faɗuwar. Hoto: DD Olusegun

Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a kan batun zamewar da ya yi ya faɗi a Dandalin Eagle Square a lokacin da yake faretin ban-girma na Ranar Dimokuraɗiyya a Abuja.

A ranar Larabar da aka yi bikin cikar dimokuraɗiyyar Nijeriya shekara 25 cif babu tsaiko ne aka ga Shugaban Ƙasar ya faɗi a cikin wani bidiyo da ya yaɗu kamar wutar daji, inda 'yan Nijeriya suka yini suna tsokaci a kansa.

Sai dai jim kaɗan bayan yin hakan ne Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu abin da ya samu Tinubu bayan faɗuwar.

A wani bidiyon na daban da mai taimaka wa Shugaba Tinubu na musamman kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun wallafa a shafin X, na liyafar cin abincin dare da aka yi a fadar gwamnati, an ga Tinubun yana mayar da martani cikin raha kan batun.

“A yau da safe, na yi ƙwambo, sai labarin ya bazu a shafukan sada zumunta. Sun rikice sun kasa fahimtar abin da ya faru, ko rawar Buga na yi ko ta Babbar riga, amma rana ce ta bikin dimokuradiyya inda na yi gaisuwar Yarabawa ta dobale.

"Ni cikakken Bayerabe ne, kuma gaisuwata ta al'ada ta Dobale na yi," Tinubu ya faɗa cikin raha, lamarin da ya sa mahalarta liyafar ma tuntsurewa da dariya.

Faɗuwa a motar a-kori-kura ta fareti

Batun faɗuwar ya jawo muhawara sosai a kafofin sada zumunta a Nijeriya, inda wasu ke jajantawa, wasu kuma suka mayar da batun na zolaya.

Shugaba Tinubu ya zame ne a lokacin da yake ƙoƙarin hawa mota ƙirar a-kori-kura wadda za ta zagaya da shi a dandalin Eagles Square, amma nan da nan masu tsaro da ke kewaye da shi suka kai masa ɗauki.

Faruwar hakan ke da wuya sai mai taimakawa Shugaba Tinubu na musamman kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya wallafa saƙo a X yana cewa ce "Shugaban Ƙasa ya yi tuntuɓe a cikin mota a wajen bikin Ranar Dimokraɗiyya na June 12 har ya zame. Dan tuntube ne kawai. Nan da nan ya miƙe ya ci gaba da zagaya dandalin da ake bikin. Babu wata matsala."

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya kuma dan takarar Shugaban Ƙasa na 2023 a jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya wallafa saƙon jaje ga Tinubu a shafin X kan lamarin, tare da wallafa bidiyon faɗuwar.

"Ina matukar jajanta wa Shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya faru da shi a lokacin da yake ƙoƙarin zagayen fareti a Ranar Dimokaraɗiyya. Ina fatan yana cikin halin lafiya."

Sai dai wasu na hannun daman Tinubun sun kalli wannan jaje na Atiku a matsayin na zolaya, har ma suka mayar masa da martani.

TRT Afrika