Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC , ta sauya tsarinta na kame da kuma ba da beli / Hoto: AFP

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa (EFCC) ta sabunta ka’idojin yin kame da kuma bayar da beli kan wadanda take tuhuma da aikata laifuka.

EFCC ta sanar da cewa daga yanzu za ta bayar da muhimmanci game da hakkokin wadanda take kamawa da kuma matakan ba da belinsu.

Shugaban hukumar Mista Ola Olukoyede ne ya ba da wannan umarni cikin sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin 31 ga watan Oktoba 2023, inda ta ce matakin ya shafi dukkan reshen hukumar da ke fadin Nijeriya.

''Daga yanzu ba a amince jami'an hukumar su karbi takardun shaida ko wasu muhimman takardu daga wanda zai tsaya wa mutumin da ake tuhuma ko aka tsare a matsayin shaidar beli ba," in ji sanarwar.

Kazalika, daga yanzu dole a yi kaffa-kaffa wajen bukatar fasfo na kasa da kasa daga wurin wanda ake tuhuma, kuma hakan ya danganta da yanayin tuhumar da ake yi masa da yanayin mutumin da kasar da yake zama, a cewar sanarwar.

Labari mai alaka: Kotu ta bai wa EFCC damar karbe gidaje 324 a Kano

“Dole sharudan belin da aka gindaya wa wanda ake tuhuma da kuma wadanda za su tsaya masa wajen ba da beli su kasance masu ma’ana kuma za su iya cika su,'' a cewar daraktan Sashen Shari’a da Laifuka na EFCC, CE Sylvanus Tahir.

Ya kara da cewa, dole ne a dakatar da ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma ba tare da wani kwakkwaran dalili na tsawon lokuta da suka wuce tanadin tsarin mulkin kasa.

''Ayyukan hukumar sun dogara ne da tanadin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara) ya bayar a sashen dokar Shari'a ta Manyan Laifuka, 2011 da kuma tsarin tanadin ayyuka na hukumar EFCC wato Standard Operating Procedures, SOP," in ji sanarwar.

An kuma gargadi jami’an Hukumar kan take hakkin wadanda ake tuhuma ba tare da wata hujja ba.

Ya yi kira kan ma'aikatan hukumar da su nuna kwarewa cikin dukkan ayyukansu, tare da jaddada cewa “lokaci ya yi da za a sami sauyi da kuma yadda ake yi hukumar mummunar fahimta."

TRT Afrika