Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa, EFCC ta ce shugaban Hukumar Alhazan Ƙasar NAHCON, Malam Jalal Arabi yana hannunta inda take gudanar da bincike a kansa.
Mai magana da yawun hukumar EFCC Dele Oluwale ne ya tabbatar wa TRT Afrika hakan a wata gajeriyar zantawa ta wayar tarho a ranar Alhamis.
"Haka ne labarin da kuka ji, shugaban NAHCON na wajenmu tun ranar Talata inda muke gudanar da wani bincike a kansa," in ji Mista Oluwale.
Amma mai magana da yawun EFCC ɗin ya ƙi yin wani ƙarin bayani a kan lamarin, yana mai cewa "ba zan ƙara komai a kan wannan ba saboda bincike muke yi har yanzu."
Sai dai rahotanni da dama a faɗin ƙasar sun ce EFCC tana zargin Malam Arabi ne da almubazzaranci da rarar kuɗaɗen Aikin Hajjin 2024 da suka kai yawan Naira biliyan 90.
Wasu rahotannin sun ce tuni har EFCC ɗin ta ƙwato Riyal 314,098 daga wajen shugaban na NAHCON da wasu manyan jami'an hukumar da ake zarginsu tare.
Ko a ranar 29 ga watan Yulin da ya gabata sai da EFCC ta gayyaci Malam Arabi don yi masa tambayoyi amma daga baya ta bayar da belinsa.